Fadar shugaban kasa ta yi wa masu son yin zanga-zangar juyin juya hali raddi

Fadar shugaban kasa ta yi wa masu son yin zanga-zangar juyin juya hali raddi

Da yammacin ranar Lahadi ne fadar shugaban kasa ta sanar da masu shirin gudanar da zanga-zangar juyin juya hali cewa zabe ne hanya mafi dace wa ga duk jama'ar da ke son canja gwnati.

Fadar shugaban kasar ta fadi hakan ne a matsayin martani ga wasu kungiyoyin matasa karkashin kungiyar "Global Coalition for Security & Democracy in Nigeria" ke shirin gudanar wa ranar Litinin, 5 ga watan Agusta.

A jerin wasu sakonni da fadar shugaban kasa ta fitar a shafinta na Tuwita, ta zargi wasu mutane da fake wa da daukar nauyin matasan dake shirin zanga-zangar domin su karbi mulki ta bayan gida.

"Fadar shugaban kasa na sane da cewa kundin tsarin mulki ya bawa 'yan kasa dama da 'yancin gudanar da zanga-zangar lumana ko da ta nuna adawa da gwamnati ce.

DUBA WANNAN: Har ila yau: Masu zanga-zanga sun mamaye ofishin AI duk da haramta zanga-zanga a Abuja

"Sai dai akwai banbanci tsakanin zanga-zangar lamana da kuma ingiza mutane domin gudanar da zanga-zangar juyin juya hali.

"Babu wanda ya san fuskokin masu shirya wannan zanga-zangar, a saboda haka muke kira ga masu daukan nauyinsu da su fito su bayyana Kansu idan har suna girmama 'yan Najeriya domin kowa ya san su," a cewar jawabin.

Sannan jawabin ya cigaba da cewa, "kimanin watanni shida da suka wuce ne Najeriya ta gudanar da zabuka a dukkan matakan takara a fadin kasa. Shugaba Buhari da jam'iyyarsa ta APC ne suka samu mafi rinjayen nasara a zabukan.

"Shugaban kasa na kira ga masu buya da sunan wannan zanga-zanga domin su samu mulki, da su fito fili su bayyana kansu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel