Sabani ya shiga tsakin Najeriya da MTN a kan tarar kudi da haraji

Sabani ya shiga tsakin Najeriya da MTN a kan tarar kudi da haraji

A Ranar Juma’a, 2 ga Watan Agusta, 2019, Kamfanin MTN da ke Najeriya, ya bayyana cewa sun samu rashin jituwa da gwamnatin tarayya a game da wasu tara da a ka ci ta a shekarar 2015.

Mista Onome Okwah, wanda shi ne babban jami’in hulda da yada labarai na kamfanin MTN da ke Najeriya ya yi magana a game da wani jawabi da hukumar karbar harajin Najeriya ta yi kwanaki.

MTN ta sha ban-ban ne da hukumar FIRS a kan kudin da a ka ci ta tara shekaru kusan hudu da su ka wuce a matsayin ukuba inda ta ke nema a sake bibiyar wannan lamarin ta fuskar shari'a.

Onome Okwah ya ke cewa sun biya hukumar FIRS wannan kudi da a ka yanke masu, sai dai su na da ja a game da wani kwamitin haraji da shugaban FIRS da Ministar kudin Najeriya ta kafa.

Okwah ya ke cewa za su jira su ga matakin da gwamnatin Najeriya za ta dauka a kan wannan lamari. “MTN za su cigaba da bin dokokin harajin Najeriya sau da kafa” Inji Jami’in kamfanin.

KU KARANTA:

Mista Okwah ya kara da cewa: “Za mu yi biyayya ga duk abin da kwamitin ta yanke. A shirye MTN ta ke da ta sauke nauye-nauyen da ke kanta domin ganin cigaban tattali da halin Najeriya”

Babban kamfanin ya sake tunawa Duniya cewa: “Daga shekarar 2001, mun kashe fiye da Tiriliyan 2 domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya, inda a ka kashe fiye da Tiriliyan 1.7 wajen biyan haraji.”

Shugaban hukumar FIRS mai karbar haraji a Najeriya, Babatunde Fowler, ya na zargin kamfanin MTN da zaftare haraji daga cikin tarar Biliyan 330 da hukumar NCC ta ci kamfanin sadarwan.

Fowler ya hakikance a kan bai kamata a cire wani haraji daga cikin kudin da MTN ta biya ba. Maganar cewa bai dace a cire haraji daga tarar da Najeriya ta ci MTN ba ne ya kawo ja-in-ja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel