Tirkashi: Abinda zamu yiwa masu kokarin juyin mulki a kasar nan - Shugaban hukumar 'yan sanda yayi gargadi

Tirkashi: Abinda zamu yiwa masu kokarin juyin mulki a kasar nan - Shugaban hukumar 'yan sanda yayi gargadi

- Hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta zargi wata kungiya mai suna 'Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria' da kokarin yin juyin mulki

- Kakakin hukumar 'yan sandan, Frank Mba, ya bayyana cewa kungiyar suna jawo hankalin 'yan Najeriya ta hanyar bidiyo da suke aikawa a shafukan sada zumunta, inda suke kira da a fito a yiwa gwamnatin tarayya juyin mulki

- Mba ya bayyana wannan shiri na kungiyar a matsayin yunkuri na ganin an canja tsarin kasar nan

Shugaban hukumar 'yan sanda (IGP) Mohammed Adamu, yayi gargadi akan shirin yin juyin mulki da wata kungiya take yi, inda ya bayyana hakan a matsayin laifi babba.

Sanarwar wacce ta fito daga bakin kakakin hukumar, Frank Mba, a ranar Asabar dinnan, 3 ga watan Agusta, ya ce kungiyar suna jawo hankalin 'yan Najeriya ta hanyar aika musu da bidiyo wanda yake dauke da manufarsu na yin zanga-zanga a ranar Litinin dinnan 5 ga watan Agusta akan gwamnatin tarayya.

Mba ya bayyana wannan shiri na kungiyar a matsayin wani kokari da na ganin an canja tsarin kasar nan, kuma irin wannan shiri laifi ne babba daidai da ta'addanci.

KU KARANTA: Zaben 2019: Gwamnatin tarayya ta aikawa Atiku Abubakar wani muhimmin sako

Kakakin hukumar ya ce jami'an tsaron kasar nan ba za su taba bari wannan abu ya faru ba, domin ba za su tsaya su sanya ido wasu mutane su nemi tada zaune tsaye a kasar nan ba.

Hukumar ta gargadi shugabannin wannan kungiya, da masu goya musu baya akan ba za ta sassautawa duk wanda ta kama da hannu a wannan lamari ba.

Mba ya kuma bukaci iyaye da su tsawatarwa da 'ya'yansu akan irin wannan lamari domin duk wanda ta kama babu sani ba sabo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel