Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, ya shiga siyasa

Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, ya shiga siyasa

Tsohon shugaba hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya tsunduma cikin siyasar Najeriya domin a dama da shi.

Tsohon Alkalin zaben ya shiga jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP) game da cewar shugaban amintattun jam'iyyar, Balarabe Musa.

Jega, wanda ya kasance shugaban jami'ar Bayero da ke Kano ya shugabanci hukumar zabe tsakanin shekarar 2010 da 2015 inda ya gudanar da zaben shugaban kasa har sau biyu.

Bayan bakin jinin da yayi a arewacin Najeriya a shekarar 2011 inda ya alanta tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Jega ya samu farin jini a shekarar 2015 inda ya alanta shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar.

Ba'a san takamamman lokacin da Jega ya shiga jam'iyyar PRP ba amma Alhaji Balarabe Musa ya bayyana cewa an fara tattaunawa da shi a watanni uku da suka gabata.

"Na fara samun labari watanni uku da suka gabata a daga bakin shugaban jam'iyyarmu cewa zai shigo jam'iyyarmu." Balarabe Musa ya laburta a daren Juma'a.

Ya siffanta wannan a matsayin babban cigaba ga jam'iyyar PRP wacce ke cikin daya daga cikin kananan jam'iyyun Najeriya.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel