Ganduje vs Abba Gida-Gida: PDP ce ta nemi a yi zaben kece raini - Yakasai

Ganduje vs Abba Gida-Gida: PDP ce ta nemi a yi zaben kece raini - Yakasai

Umar Tanko Yakasai, jami'in tattara kuri'u na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano ya ce jam'iyyarsa ne ta bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta soke sakamakon zaben mazabar Gama a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris.

A yayin da ya ke amsa tambayoyi a kotun sauraron karar zaben gwamna da ke zaman ta a Miller road, Yakasai ya ce yana daga cikin wadanda suka amince da soke sakamakon wasu rumfunan zabe a mazabar Gama inda aka samu rikici yayin zaben.

A cewar shi, an samu matsaloli kama jefa kuri'u fiye da adadin mutanen da aka tantance a wasu rumfunan zabe a Gama hakan ya za wakilan jam'iyyar da ke rumfunan zaben suka rattaba hannu kan takardan soke sakamakon zaben wanda hakan ne ya janyo INEC ta bukaci a yi zaben raba gardama a ranar 23 ga watan Maris.

DUBA WANNAN: Shahararrun 'yan wasa 15 da ba su taba buga wa kasarsu ta haihuwa kwallo ba

Ya kuma shaidawa kotun zaben cewa da hannunsa ne ya rattaba hannu kan takardar da sauran wakilan jam'iyyar suka bayar da amincewarsu na soke zaben.

Ya ce rikici ya barke yayin da ake kadiya sakamakon zaben gwamna a karamar hukumar Nassarawa wadda hakan ya janyo wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka kone ainihin takardan sakamakon zabe na INEC.

"Haka ya sa na kwashe kayayakin zaben da su kayi saura na rufe kai na da kayan zaben a wani daki da ke kusa da mu," a cewar Yakasai.

A yayin da ya ke amsa tambayoyi daga lauyan Gwamna Ganduje, Offiong Offiong (SAN), Yakasai ya ce bai mika wa jami'an INEC kayayakin zaben ba har sai da ya jira misalin mintuna 30 bayan rikicin ya kare kafin ya tafi da kayan zaben hedkwatan ofishin 'Yan sanda da ke Bompai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel