Babu dan Najeriyar da zai yi da na sanin sake zabar Buhari – Omo-Agege

Babu dan Najeriyar da zai yi da na sanin sake zabar Buhari – Omo-Agege

-Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya ce babu dan Najeriyan da zai yi da na sanin sake zaben Shugaba Buhari

-Omo-Agege ya fadi wannan maganar ne a mahaifarsa dake karamar hukumar Ughelli ta arewa a jihar Delta

-Omo-Agege shi ne dan Kudu maso kudu na farko da ya samu damar hawa kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa tun shekarar 1999

Mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege ya ce babu dan Najeriya babba ko yaro da zai yi da na sanin sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu, domin Shugaban kasan na da manufar kawo gyara a kasar nan.

Omo-Agege ya ce, kasancewarsa mataimakin Shugaban majalisar dattawa na da nasaba da sa hannun Shugaba Buhari da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.

KU KARANTA:Wike ya tsige Shugaban Jami’ar Rivers

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis a kauyensa na Orogun dake karamar hukumar Ughelli ta arewa cikin Jihar Delta a lokacin da aka yi masa tarba ta musamman lokacin da ya sauka garin.

Tun bayan da aka zabe shi a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa, wannan ne karo na farko da Omo-Agege ya ziyarci kauyen nasa. Sanata Omo-Agege shi ne ke wakiltar Delta ta tsakiya a majalisar dattawa.

Har ila yau, Sanatan ya isa garin nasa ne tare da dan takarar gwamnan APC a jihar Cif Great Ogboru tare da Shugaban APC a jihar Jones Erue da kuma wasu manya-manyan ‘yan APC a jihar ta Delta.

Isowarsa tare da Ogboru ta zama sanadiyar korar wata jita-jita da ke yawo cewa basu ga maciji da shi da dan takarar gwamnan.

Omo-Agege ya ce: “ Dukkaninku kun san yadda na samu wannan matsayi na mataimakin shugaban majalisar dattawa, abinda yankinmu na kudu maso kudu bai taba samu tun shekarar 1999.

Amma sai ga shi a yau mun samu. Goyon bayan Shugaba Buhari ne ya kaimu ga wannan nasara. Dama na fadi maku idan kuka zabe ni da Buhari ba zaku yi da na sani ba, saboda Buhari na kaunar kabilar Urhobos da ma ‘yan Najeriya baki daya.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel