Sarkin Donga ta jihar Taraba ya rasu

Sarkin Donga ta jihar Taraba ya rasu

Mun samu labarin rasuwar Sarkin Donga Dr Dakuma Stephen Banyonga. Sarkin mai daraja ta daya ya rasu ne ranar Alhamis a wani asibiti dake Abuja.

Shugaban karamar hukumar Donga, Mista Nashuka Musa Donga ne ya tabbatar da labarin rasuwar a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarho.

KU KARANTA:Gwamnatin tarayya ta tsamo ‘yan Najeriya miliyan 5 daga matsanancin talauci a shekara 3 – Buhari

Shugaban ya kara fadin cewa, cikakken bayanin rasuwar zai zo daga baya duk da cewa mutane da dama sun riga sun ji labarin rasuwar Sarkin wadda ta zo kunnunwansu kwatsam.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel