Hukumar Kwastan ta damke kaya na kimanin naira biliyan 1.5 a jihar Kaduna

Hukumar Kwastan ta damke kaya na kimanin naira biliyan 1.5 a jihar Kaduna

Hukumar kwastan reshen Zone B a jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kama kayayan day a kai kimanin naira biliyan 1.5 a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuni a jihar

Shugaban hukumar a jihar Mustapha Sarkin-Kebbi, ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a garin Kaduna inda ya kara da cewa kamun da hukumar ta yi bana ya zarce bara.

A lissafe dai hukumar ta yi kame sau 623 a tsakain watanni shida da suka gabata sannan a tsakanin wannan lokaci hukumar ta kama motoci 153, buhunan shinkafa 8,168, katan din taliya 820, buhunan siga 167, dila gwanjo 147, jarkunan man gyada 1,035, tayoyin motoci 333 da kwalayen Tramado 1,550.

Sarkin-Kebbi yace sun kuma kama mutanen 14 da suke da hannu a shigo da wadannan kaya inda daga ciki biyu an yanke musu hukunci sannan hudu na jiran kotu ta yanke musu hukunci.

KU KARANTA KUMA: Sallah: Kada ku ci bashi don siyan ragon layya – Malamai sun yi gargadi

Ya kuma ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta gudanar da aiyukkan ta yadda ya kamata.

Daga karshe ya kuma yi kira ga sauran hukumomi a kasar nan kan mara wa hukumar baya wajen wayar da kan mutane game da illar yin fasakwaurin abubuwan da gwamnati ta hana shigowa da su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel