Buhari ya lissafa sabbin hanyoyi 5 da gwamnatinsa za ta bi don magance kallubalen tsaro

Buhari ya lissafa sabbin hanyoyi 5 da gwamnatinsa za ta bi don magance kallubalen tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Laraba ya lissafa wasu matakai da gwamnatinsa za ta dauka domin kawo karshen kallubalen tsaro da ke adabar kasar.

Wasu daga cikin matakan sun hada da kara daukan sabbin jami'an tsaro da saka na'urar nadab bidiyo na 'CCTV' a manyan tituna da muhimman wurare domin tona asirin wadanda ke aikata laifuka a wuraren.

Buhari ya lissafa wadannan abubuwan ne yayin ganawarsa da wasu masu sarautun gargajiya daga yankin Kudu maso Yamma na kasar a Abuja.

Shuagaban kasar ya yi cikakken bayanin matakan tsaron da gwamnatinsa za ta dauka a shafinsa na Twitter.

Ga wasu abubuwan da shugaban kasar ya lissafa:

1 - Zamu dauki karin 'yan sanda kuma mu ajiye su a garuruwansu da kananan hukumominsu

2 - Zan bayar da umurni a bawa jihohi lasisin samun jirgi mara matuki domin amfani dashi wurin leken asiri a dazukkan da masu aikata laifi ke buya

3 - Za mu saka na'uarar daukan hotunan bidiyo na 'CCTV' a manyan tituna da muhimman wurare domin gano wadanda ke aikata laifi da daukan mataki a kansu

4 - Za muyi aiki da gwamnatocin jihohi domin bawa 'yan sandan mu kayayyakin yaki da masu laifi na zamani

5 - Za mu cigaba da gayyato sojojin mu su rika taimakawa 'yan sanda idan bukatar hakan ya taso tare da amfani da sojojin saman wurin jefa bama-bamai a wuraren da aka gano bata gari na buya

Sanarwar ta shugaban kasar ta kuma ce: "Ina tabbatarwa 'yan Najeriya cewa za mu cigaba da hukunta masu laifi domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga dukkan 'yan Najeriya. Hakan ne zai taimaka mana a gwamnatance kuma zai amfani mutanen da suka zabe mu.

"Mun san cewa sai da tsaro za mu iya cikawa al'umma alkawurran da muka dauka musu. Hasali ma ba za a iya samun cigaba ba idan babu tsaro. Wannan sako ne ga dukkan mu domin mu tashi mu nemo hanyoyin tabbatar da tsaro a kasar mu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel