Kyanda: An samu mutane 21,011 da cutar a Arewa maso gabas inda 100 suka mutu – Bincike

Kyanda: An samu mutane 21,011 da cutar a Arewa maso gabas inda 100 suka mutu – Bincike

-Cutar kyanda ta kama dubban mutane a jihohin Arewa maso gabashin Najeriya

-Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Borno Sule Mele ne ya bamu wannan labari ta hannun kamfanin dillacin labaran Najeriya

-Jihar Adamawa ba ta samu bullar cutar ba ko daya kamar yadda binciken ya sanar da mu

Jihohin yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun samu jimillar mutum 21,011 wadanda suka kamu da cutar kyanda yayin da mutane 100 suka mutu a cikin ‘yan watannin da suka gabata.

Wani bincike da Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN yayi ya tattaro mana cewa, yayin da ake samun bullar wannan cuta a jihohin Bauchi, Borno, Yobe da Gombe, jihohin Adamawa da Jigawa sun bayyana shaida mana cewa cutar ba ta bayyana ba garuruwansu.

KU KARANTA:Yahaya Bello ya faranta ran ma'aikatan Kogi, ya biya su albashin watanni 5

Daraktan Hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Borno, Sule Mele ya ce, an samu mutum 18,204 da cutar kyanda a bangarori daban-daban na jihar daga tsakanin watan Janairu zuwa yanzu. Mutum 93 suka mutu kuma akasarinsu yara ne kanana.

Haka zalika, ya danganta yaduwar cutar musamman a sansanin ‘yan gudun hijira bisa rashin isassun kayan kula da lafiya, a sakamakon rikicin ‘yan Boko Haram dake addabar yankin.

Mele, a matsayinsa na kwararren likita ya bayyana mana cewa “ Rashin samun rigafi ga akasarin mutanen ne ya sanya cutar ta kama su.

“ Rikicin Boko Haram ne ke hana jami’in ma’aikatar lafiya shiga wadannan wuraren domin yiwa al’umma allurer rigafin kyanda.”

Rahotanni sun nuna mana cewa, hukumar kula da lafiya ta matakin farko a jihar Borno, ta fara fitar da sabbin tsare-tsare domin tabbatar da jama’a sun samu allurar rigafi da kuma taimako na musamman da suke bukata wurin kaucema wannan cuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel