Hatsarin mota ya janyo mutuwar mahaifiya da jaririyarta a Legas

Hatsarin mota ya janyo mutuwar mahaifiya da jaririyarta a Legas

Wata jaririya Chimbusomma Uligwe, ta yi kacibus da ajali bayan wani direban babbar motar haya ya buge mahaifiyarta, Tochukwu kuma ya kama gaban sa ba tare da tsayawa ba.

Jami'an tsaro na 'yan sanda bisa jagorancin Janah Jatau, wani dan sanda mai jiran ko ta kwana, sun kurewa direban wannan mota gudu a kan hanyar Lekki daura da tashar Elf a karamar hukumar Eti-Osa. An yi nasarar damke direban tare da karen motar sa.

Mummunan hatsarin da ya auku ya yi sanadiyar mutuwar Tochukwu nan take inda kuma daga bisani jaririyar ta tabi sahunta kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jaridar Punch Metro ta ruwaito cewa, wannan mugun ji da mugun gani ya auku a ranar Laraba, 9 ga watan Yunin 2019, kwana guda gabanin cikar Chimbusomma shekara guda a doron kasa.

KARANTA KUMA:

Wani mai bayar da shaida, Ukamaka, ya ce direban motar mai lamba APP 584 XX ya arce tare da karen motar sa domin gudun shiga hannun hukuma.

Makonni biyu da suka gabata wata sabuwar amarya tare da angonta da kuma wasu mutane 3 sun riga mu gida a sanadiyar wani mummunan hatsarin mota da ya auku a babbar hanyar Abeokuta zuwa Ibadan cikin karamar hukumar Odeda ta jihar Ogun.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel