Buhari, Oshiomhole da Omo-Agege sun kebance a fadar Villa

Buhari, Oshiomhole da Omo-Agege sun kebance a fadar Villa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 29 ga watan Yulin 2019, ya gana a bayan labule tare da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole cikin fadar Villa dake garin Abuja.

Jim kadan bayan isowar Oshimohole fadar shugaban kasa da misalin karfe 3.25 na Yamma, ganawa da fara gudana tsakanin sa da shugaban kasar kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

An kiyasta cewa ganawa na gudana tsakanin shugaban kasa Buhari da kuma tsohon gwamnan jihar Edo domin tattauna batutuwa a kan sha'anin jam'iyya mai ci ta APC da kuma kokarin ciyar da ita gaba.

Kazalika shugaban kasar a fadar sa ta Villa ya shiga bayan labule tare da mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ovie Ome-Agege.

A yayin da har wa yau ganawa ke ci gaba da gudana a tsakanin su, jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Omo-Agege ya isa fadar shugaba Buhari da misalin karfe 2.35 na Yammacin Litinin.

KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 4 a Taraba

A wani rahoton na daban da jaridar Legit.ng ta ruwaito, majalisar dattawan Najeriya a ranar Litinin ta ci gaba da tantance zababbun ministocin Buhari wanda ta fara a ranar Laraba 24 ga watan Yuli.

Majalisar bayan zamanta na ranar Juma'a ta makon jiya, ta tantance zababbun ministoci 31 cikin 43 da shugaban kasa ya gabatar mata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel