Buhari Vs Atiku: Ba zamu gabatar da shaidun mu ba, shaidun Atiku sun gama yi mana aiki - INEC

Buhari Vs Atiku: Ba zamu gabatar da shaidun mu ba, shaidun Atiku sun gama yi mana aiki - INEC

A ranar Litinin ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta shaida wa kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa cewa babu bukatar ta gabatar da shaidu domin kare kan ta, saboda shaidun da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, ya gabatar sun gama wanke ta daga dukkan wani zargi da masu kara ke yi mata.

Atiku da jam'iyyarsa, PDP, na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019, wanda INEC ta bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na jam'iyyar APC ne ya samu nasara.

Kotu ta cigaba da zamanta ne a ranar Litinin domin hukumar INEC ta fara kare kan ta bayan msu kara sun kammala gabatar da korafinsu da gabatar da shaidu 62 a ranar 19 ga watan Yuli a gaban kotun mai alkalai guda biyar karkashin jagorancin Jastis Mohammed Garba.

Amma da aka kira Yunus Usman (SAN), babban lauyan hukumar INEC, a zauren kotun, sai ya ce ba dole ba ne su gabatar da wata shaida domin kare kan su saboda shaidun da masu kara suka gabatar sun gama wanke hukumar INEC daga amsoshin tambayoyin da suka bayar lokacin da ya yi musu tambayoyi.

"Mai girma, mai shari'a, ba zamu bata lokacin wannan kotu mai girma ba ta hanyar kiran shaidun mu ba. Shaidun da masu kara suka gabatar sun riga sun wanke hukumar INEC daga dukkan zargin da masu kara ke yi mata dangane da korafe-korafen da suka gabatar.

DUBA WANNAN: Abba Vs Ganduje: Kotu ta hana wani dan Kwankwasiyya bayar da shaida

"Amsoshin tambayoyin da suka bayar lokacin da suke amsa tambayoyi na sun gama kore duk wata bukata ta mu gabatar da shaidun mu, gabatar da wasu shaidu zai zama tamkar kokarin bata lokacin kotu da alkalanta ne," in ji lauya Usman.

Bayan lauyan masu kara, Dakta Livy Uzokwu, ya yi wa lauyan INEC godiya bisa yanke shawarar kin gabatar da shaidu, kotun ta daga zamanta zuwa ranar Talata domin fara sauraron Cif Wole Olanipekun, lauyan da ke kare shugaba Buhari.

Kazalika, lauyan jam'iyyar APC, Lateef Fagbemi (SAN) ya ce shawarar ya kira shaidu ko sabanin hakan ta dogara da irin matakin da lauyan Buhari ya dauka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel