Manyan daliliai uku da suka tilasta Buhari ya fasa bawa Ambode minista

Manyan daliliai uku da suka tilasta Buhari ya fasa bawa Ambode minista

Tun bayan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fitar da jerin sunayen mutane 42 da yake son bawa mukamin minista ake mamakin rashin ganin sunayen wasu jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC, musamman tsofin gwamnonin ta.

Daga cikin irin wadannan mutane da ake mamakin rashin ganin sunan su akwai tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, wanda ake ganin na da daurin gindi a fadar shugaban kasa.

Wata majiyar fadar shugaban kasa ta bayyana cewa dole ce ta saka shugaba Buhari ajiye Ambode saboda irin sukar da saka sunan tsohon gwamnan ta jawo daga jihar da ya fito. Majiyar ta kara da cewa nada Ambode a matsayin minsta za ta jawo baraka tsakanin shugaba Buhari da wasu sahibansa daga jihar Legas.

Dukkan dalilan da suka tilasta Buhari fasa bawa Ambode minista na da alaka da jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, wanda ya kasance dan siyasa mafi karfi a yankin kudu maso yamma na 'yan kabilar Yoruba.

Matsala ta farko da ta jawo Tinubu ya nuna adawa da bawa Ambode minista ita ce yadda tsohon gwamnan ya garzaya fadar shugaban kasa domin neman ta dakatar da Tinubu daga yunkurin hana shi sake komawa kujerar gwamnan jihar Legas, laifin da majiyar mu ta bayyana mana cewa Tinubu ya ci alwashin ba zai yafe wa Ambode ba kuma zai nuna masa cewa hatta a fadar shugaban kasan shine keda kumbar susa.

DUBA WANNAN: Omu Anioma: Sarautar kabilar Igbo da ke mayar mace namiji har ta auri mace su haifi yara

Duk da shugaba Buhari ba zai rasa wani abu ba idan ya nada Ambode a matsayin minista, sai dai yana bukatar goyon bayan Tinubu wajen ganin cewa mutanen yankin kudu maso yamma basu juya masa baya ba, saboda matsalar da ta kunno kai tsakanin kungiyar Afenifere da Fulani makiyaya.

Shugaban kasa ya dogara da Tinubu wajen lallashin dattijai da shugabannin al'ummar kabilar Yoruba da kuma canja fahimtar jama'ar yankin a kan kallon ta'addanci da suke yi wa Fulani makiyaya, wanda Tinubu kan iya ajiye wannan aiki idan Buhari ya nada Ambode minista.

Matsala ta uku ita ce zargin da ake yi wa Ambode na cin dunduniyar jam'iyya da kuma nuna rashin da'a ga na gaba da shi.

Tun bayan hawan Oshiomhole kujerar shugabancin jam'iyyar APC yake nuna cewa dole a cigaba da amfani da tsarin siyasar ubangida a matakin tarayya da na jihohi, lamarin da ya jawo uwar jam'iyya ma ta nuna adawar ta da bawa Ambode minista duk da gatan da yake da shi a fadar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel