Yadda yaro dan shekara 7 ya zama gwamna a wata jihar kudu

Yadda yaro dan shekara 7 ya zama gwamna a wata jihar kudu

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli ya sauka daga kujerarsa domin ba wani dan shekara bakwai Daniel Olutope damar zama gwamnan jihar na kwana daya.

Daniel, dalibin makarantar St. Michael African Primary School, Ado-Ekiti ya samu damar zama gwamnan jihar ne bayan Fayemi ya ziyarci makarantarsa.

Fayemi ya kai wani ziyarar bangirma makarantar su Daniel a ranar 7 ga watan Mayu, 2019.

Daniel yayi hira dashi cike da hikima da har sai fa Fayemi ya tambaye shi ko zai zama abokinsa sannan ya kai masa ziyara gida.

Daniel ya samu rakiyar mahaifiyarsa, Misis Oluwatoyin Olutope da malamarsa, Misis Dupe Adeosun zuwa ofishin gwamnan a Ado-Ekiti.

Misis Olutope tace ziyarar “ya kasance bazata a gare ta sannan tana murnar ganin danta zaune akan kujerar gwamnan, alama da ke nuna cewa danta na iya zama gwamna a nan gaba kamar Dr Kayode Fayemi.”

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai daga zuwa kasar Liberia don halartar taro da kuma karbar wata muhimmiyar kyauta a kasar

Misis Adeosun ta kuma yaba ma gwamnan akan gayyatarta tare da yaron, inda ta bayyana cewa wannan karamcin zai karfafa gwiwar malamai da kuma yaran wajen kokarin ganin sun zama wasu a nan gaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel