Majalisar Dattawa zata tantance Sylva, Magashi, da mutane 6 a yau

Majalisar Dattawa zata tantance Sylva, Magashi, da mutane 6 a yau

-Shugaban Majalisar ya lissafa sauran kamar haka; Richard Adeniyi Adebayo (Ekiti), Mustapha Baba Shehuri (Borno), Ramatu Tijjani (Kogi), Mohammed Abdullahi (Nasarawa), Tayo Alasoadura (Ondo), da kuma Sunday Dare (Oyo)

-Tantancewar jiya, wacce ta kwashe tsawon awa shidda, Sanatocin sun tantance mutane 10

- Shidda daga cikin mutanen sun samu kulawa ta musamman inda akace suyi ruku’i su tafi

Majalisar Dattawa zata tantance Manjo janar Bashir salihi Magashi (Kano), Timipre Sylva (Bayelsa) da kuma mutane shidda, a yau, inji Shugaban Majalisar Dattawa.

Ya lissafo sauran daza a tantance a yau wanda suka hada da Richard Adeniyi Adebayo (Ekiti), Mustapha Baba Shehuri (Borno), Ramatu Tijjani (Kogi), Mohammed Abdullahi (Nasarawa), Tayo Alasoadura (Ondo), da kuma Sunday Dare (Oyo).

A zaman jiya, wanda ya kwashe tsawon awa shidda, Sanatocin sun tantance mtane 10. Shidda daga ciki sun samu kulawa ta musamman inda akace suyi ruku’i su tafi.

Mutanen sune Sen Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Rotimi Amaechi (Rivers), Uchechukwu Ogah (Abia), Sen George Akume (Benue), Ogbonnaya Onu (Ebonyi), Emeka Nwajiuba (Imo), Sen Adeleke Mamora (Lagos), Olamilekan Adegbite (Ogun), Adamu Adamu (Bauchi) da kuma Sharon Ikeazor (Anambra).

Anfara tantancewar da Karfe 11:20 na safe inda aka fara da Ogah, dan Jihar Abia, angama da misalin karfe 6:10 na yamma da Ikeazor dan Jihar Anambra. Sanatocin sunje hutun awa daya (1 zuwa 2 na yamma).

Mutane da akace suyi ruku’i su tafi sune Akpabio, Amaechi, Akume, Nwajuaba, Mamora da kuma Ikeazor, bayan sunyi gajeren jawabi kamar yadda Al’adar Majalisar take.

Akume ne mutumin farko da aka bawa kulawa ta musamman bayan da Sanata Emmanuel Oker-jev (Benue, PDP) ya bukaci da yayi ruku’i ya tafi.

KARANTA WANNAN: Borris Johnson ya sallami ministan kudin Birtaniya

Lokacin da akazo kan Amaechi, sai Sen Danjuma Goje yace bai kamata tsohon Ministan ya samu kulawa ta musammanba domin kuwa shi tsohon dan majalisar jahohi ne.

Goje yace “dokokin mu babu Majalisar Dokoki.”

Sai dai Lawan yace”na yarda a dokarmu babu Majalisar dokoki amma zamu barshi yaci albarkacin tare".

Haka kuma Sanatoci ukku daga Jihar Rivers sunyi kira da Amaechi yayi iyakar yinshi wajen samun zaman lafiya a jihar. Sun kuma bukaci da abashi Maikatar sufuri.

Da yake Magana shugaban dattawan Majalisar, Sen Yahaya Abdullahi (APC, Kebbi) yayi kira da abawa Amaechi Ma’aikar sufuri, ya kumace ya kamata ya duba aikin layin dogo na Arewa maso kudu na Jihohin Zamfara, Sokoto da Kebbi.

Amma sauran mutanen Mamora da Ikeazor ance suyi ruku’I su tafi ba tareda wani daga cikin Sanatoci yayi korafi ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook:https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel