Yadda wani likitan Najeriya da yaje aikin Hajji ya ceto rayuwar Balarabe da yake kakarin mutuwa a Masallacin Annabi

Yadda wani likitan Najeriya da yaje aikin Hajji ya ceto rayuwar Balarabe da yake kakarin mutuwa a Masallacin Annabi

- Wani mutumi da ya fadi a cikin Masallacin Annabi da ke birnin Madina bayan kammala sallar Magariba, an ceto rayuwarshi ta bayan wani likita dan Najeriya ya kai masa dauki

- Mutumin wanda ya fadi babu shiri ya samu taimakon wani likita da yake aiki a hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Legas

- Bayan fama da ma'aikatan taimakon gaggawa na kasar suka yi basu samu nasara ba, likitan ya gwada sa'ar sa kuma cikin ikon Allah mutumin ya tashi

A daren ranar Litinin ne Wani mutumi ya fadi bayan an kammala Sallar Magariba, wacce ake yi da misalin karfe 7 na dare. Ma'aikatan taimakon gaggawa na bangaren lafiya a kasar ta Saudiyya an hango su suna ta faman neman hanyar da za su ceto rayuwar wannan mutumin.

Mutumin ya dawo hayyacinsa ne, bayan wani ma'aikacin jaridar The Nation kuma ma'aikaci a bangaren lafiya a hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Legas (LSMPWB), Dr Abideen Aro ya isa wajen.

Aro ya bayyanawa ma'aikatan cewa shi ma'aikacin lafiya ne kafin su barshi ya taba mutumin. Cikin gaggawa ya nemo wasu kayan aikin da zasu taimaka masa wajen gano halin da mutumin yake ciki.

KU KARANTA: Kowa ya debo da zafi bakinsa: 'Yan coci sun yiwa Faston su dan karen duka

Bayan dan wani lokaci mutumin ya bude idonsa, alamun ya farfado, inda daga nan aka yi gaggawar garzayawa dashi zuwa asibiti domin karbar magani. Ma'aikatan taimakon gaggawar sun yiwa Dr Aro godiya sosai da irin kokarin da yayi.

A cewar Dr Aro, wanda yake aiki a bangaren hadarurruka na jihar Legas, ya ce ruwan jikin mutumin ya kare ne. Ya ce yanayin zafin da ake a kasar ta Saudiyya shine ka iya jawo wannan matsalar. Aro wanda yake tsohon ma'aikaci ne a asibitin koyarwa na jihar Legas, ya ce mutumin yana bukatar a kara masa ruwa domin karfin jikinsa ya dawo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel