Ambrose Owuru ya fadawa Kotu cewa shi ya lashe zaben 2019

Ambrose Owuru ya fadawa Kotu cewa shi ya lashe zaben 2019

‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta Hope Democratic Party (HDP), Mista Ambrose Owuru, ya fito ya na ikirarin cewa ya doke shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben bana.

Ambrose Owuru, ya ke cewa ya ba shugaba Muhammadu Buhari wanda a ka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, ratar kuri’a fiye da miliyan 50 a zaben raba gardaman.

‘Dan takarar ya yi wannan jawabi ne ta bakin wani daga cikin manyan kusoshin jam’iyyarsa ta Hope Democratic Party watau Yusuf Ibrahim. Ibrahim ya fadawa kotu cewa HDP ce ta yi nasara.

A cewar wannan Jigo na HDP, ‘dan takarar shugaban kasar na sa ya samu nasara ne a raba-gardaman da a ka shirya a kasar a Ranar 16 ga Watan Fubrairun 2019, ko da ba ayi zabe a ranar ba.

KU KARANTA: Hannun ka ba ya rubewa ka cire ka jefar a ke yi da Arewa a mulkin nan - Sani

Idan ba ku manta ba, hukumar zabe mai zaman kan-ta a Najeriya watau INEC, ba ta gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fubrairun da a ka shirya, saboda wasu dalilai da ta bayyana.

Sai dai duk da haka, jam’iyyar HDP mai hamayya ta na da’awar ta samu nasara a zaben raba-gardaman shugaban kasa da mutane su ka kada, har da kira a ruguza babban zaben na 2019.

Wannan jam’iyya ta shigar da kara gaban kotu ta Lauyanta, Eze Nnanyelugo, inda har wa yau ta ke cewa dakatar da zaben shugaban kasa na bana da a ka yi ya sabawa doka da tsarin Najeriya.

Nnanyelugo, wanda shi ne babban Lauyan jam’iyyar HDP ya yi wannan bayani ne a Ranar 22 ga Watan Yuli, 2019, lokacin da ya bayyana gaban kotu ya na mai kalubalantar zaben da APC ta ci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel