Jerin ministoci: Yakasai ya yiwa Buhari wankin babban bargo

Jerin ministoci: Yakasai ya yiwa Buhari wankin babban bargo

Wani babban jigon arewa, Tanko Yakasai ya caccaki jerin sunayen ministocin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saki a ranar Talata, 23 ga watan Yuli, inda ya bayyana cewa ya bata tsarin kudirin gwamnati akan yaki da cin hanci da rashawa.

Da yake martani kan sunayen, Yakasai ya kara da cewa babu wani kwakwaran dalili a kan jinkirin da aka samu wajen nadin ministocin, duba ga cewar sunayen da aka gabatar na dauke da mafi akasarin tsoffin yan majalisar Shugaban kasar.

“Jerin sunayen sabbin ministoci da Shugaban kasar ya gabatar a gaban majalisar dattawa sun isa wakilci, amma sai dai zabar wasu mutane da ke makale da guntun kashi na rashawa cin fuska ne ga yaki da cin hanci da rashawar da Shugaban kasar ke yi.

KU KARANTA KUMA: Abun da ya kamata ku sani game da zababbiyar ministar Buhari, Sadiya Umar Farouq

“Tunda dai akwai tsoffin ministoci da dama da suka dawo sabon gwamnatinsa, hakan na nufin ba za a samu banbanci ba sosai a tsakanin sabuwar gwamnati da ta baya.

“Abun da na kula shine ganin cewa Shugaban kasar ya rigada ya san mafi yawacin zababbun ministocin, babu wani dalili a jinkirin da aka samu wajen gabatar da sunayen,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel