Iska mai karfi hade da ambaliyar ruwa ta kashe mutane 4, ta lalata gidaje 3201 a Zamfara

Iska mai karfi hade da ambaliyar ruwa ta kashe mutane 4, ta lalata gidaje 3201 a Zamfara

Wani kiyasi ya nuna cewa a kalla gidaje dubu dari uku da dari biyu da wani mutum guda ne ambaliyar ruwa da iska mai karfi suka shafa kai tsaye a kauyuka 21 da ke kananan hukumomin jihar Zamfara 6.

Sunusi Muhammad Kwatarkwashi, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Zamfara, ne ya sanar da hakan ga majiyar Legit.ng.

Kwatarkwashi ya bayyana cewa annobar ta kashe mutane hudu, da suka hada da soja guda da dan sanda, daga ranar 6 ga awatan Yuni zuwa ranar 17 ga watan Yuli na shekarar nan.

A cewarsa, annobar ta shafi gidaje, ta hanyar rushe su ko yin awon gaba da rufinsu, tare da raba mutane da gidajensu da lalata musu kayan amfani masu yawa.

DUBA WANNAN: Kan 'yan majalisar wakilai ya rabu a kan sakin Zakzaky, sun kada kuri'a a sirrance

Ya kara da cewa annobar ta lalata dukiya ta miliyoyin kudi a kauyuka 21 da ke kananan hukumomin Talatar Mafara, Bungudu, Maru, Anka da Gusau.

Kwatarkwashi ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki matakan kiyaye faruwar irin wannan annoba a nan gaba.

Ya yi kira ga mutanen jihar da su guji gina gidaje a kan magudanan ruwa da suke gyara magudansu na ruwa domin bawa kokarin gwamnati na ceton rayuka da kare dukiyoyin jama'a goyon baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel