Dalilin da ya sa Arewa ke hakuri da Buhari - Shehu Sani

Dalilin da ya sa Arewa ke hakuri da Buhari - Shehu Sani

Tsohon dan majalisa mai wakiltan mazabar Kaduna Ta Tsakiya a Majalisar Tarayya, Shehu Sani ya yi ikirarin cewa al'ummar Arewa suna hakuri da salon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ne saboda daga yankinsu ya fito.

Sani ya yi wannan furucin ne a wurin wani taro da aka gudanar a ranar Litini a Kaduna.

Ya ce yankin Arewa ba ta dauki wani mataki kwakwara kan Buhari ba duk da kashe-kashe da asarar dukiyoyi da ake yi a Arewa.

Ya koka kan koma bayan ilimi da tsananin talauci da yankin ke fama da shi inda ya yi kira ga Shugaban kasar ya dauki mataki cikin gaggawa.

DUBA WANNNAN: Buhari zai dauki sabbin matakan tsaro bayan kisan mutane 37 a Sokoto

Tsohon jigon na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya ce, "Al'ummar Arewa suna hakuri da gwamnati ne a yanzu saboda Buhari ke mulki kuma shi ma dan arewa ne kamar su.

"A lokacin da dan Kudu ke mulki, 'yan Arewa suna cacakar gwamnati idan tayi ba dai-dai ba amma da dan arewa ya hau mulki sai muyi shiru.

"Muna kunya, muna takatsantsan. Muna tsoron fadi cewa titunan mu sun lalace a Arewa. Mun fi kwazon fadin gaskiya idan shugaban ba dan Arewa bane.

"Idan an kashe mutane a Kudu ne za ka ji anyi magana fiye da yadda ake yi idan hakan ya faru a Arewa saboda su 'yan kudu suna kallubalantar shugaban kasa ya yi aikinsa. Mu nan a Arewa, shiru ake yi saboda muna jin kunyan fada. Suna ganin kamar Buhari baya laifi."

Sani ya bayar da misalin yadda kisar diyar Pa Fasoranti ya zama babban lamari a kasar fiye da sauran kashe-kashen da ake yi a sauran jihohin arewa da kuma yadda shugabanni da 'yan siyasar Kudu da Yamma suka saka baki cikin lamarin.

Ya shawarci shugaban kasar ya rika sauroron shawarwarin mutane ko da baya kaunar su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel