An saki mutane 200 da aka yi garkuwa dasu a jihar Zamfara

An saki mutane 200 da aka yi garkuwa dasu a jihar Zamfara

-Komishinan yan sandan jihar Zamfara Usman Nagogo yace an sako mutane 200 bayan zaman sulhu da aka yi da masu garkuwa da mutane da sauran yan ta’adda na tsawon makonni ukku.

-“Yawan mutanen da aka kubutar a kwanaki shidda sun kai mutum talatin da ukku. Hakan ya nuna sulhun yana aiki a jihar”, kamar yadda yace.

Komishinan yan sandan jihar Zamfara Usman Nagogo yace an sako mutane 200 bayan zaman sulhu da aka yi da masu garkuwa da mutane da sauran yan ta’adda na tsawon makonni ukku.

Nagogo ya shaida hakan ga manema labarai akan zaman sulhu da aka yi tsakanin yan ta’adda da yan sa kai a jihar.

“Yawan mutanen da aka saki a kwanaki shidda sun kai mutum talatin da ukku. Hakan ya nuna sulhun yana aiki a jihar”, kamar yadda yace.

KARANTA WANNAN: Jerin sababbin ministoci na karon farko guda 30

Kuma yace yawan hare-hare sun ragu sosai

Shekaran jiya ne mu ka kawo maku labarin cewa kwamandan yan ta’adda na karamar hukumar Birnin-Magaji ya amince da tsagaita ta’addanci a taron sulhu wanda gwamnatin jihar zamfara hadin gwiwa da jami’an tsaro ta shirya. Ya kuma ce jama’ar da ta’addancin ya raba da muhallansu za su iya komawa gidajen su.

Yarje-jeniyar ta gudana a fadar Mai martaba Sarkin Binin Magaji, wanda suka halarci zaman sulhun sun hada da kwamandan yan ta’adda, shugaban Fulani, shugaban yan sakai da yan sunturi da kuma kwamishinan yan sanda Usman Nagogo.

Mai Magana da yawun yan ta’addan Nasharawi yace yanzu manoma za su iya komawa gonakin su, dama sauran mutane za su iya komawa hidimomin su.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook:https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel