Karin albashi: Neman abin da ba zai yiwu ya ke kawo cikas – Oyo - Ita

Karin albashi: Neman abin da ba zai yiwu ya ke kawo cikas – Oyo - Ita

Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ta Najeriya, HoCSF, Misis Winifred Oyo-Ita, ta bayyana cewa wasu bukatu marasa bullewa da kungiyoyi ke kawowa gwamnati ya na jawo mata cikas.

Winifred Oyo-Ita ta ce akwai laifin wadannan kungiyoyi na manyan Ma’aikata wajen gaza cin ma yarjejeniyar biyan sabon mafi karancin albashi domin kuwa su na neman abin da ba zai yiwuwa.

A Ranar Litinin dinnan, 22 ga Watan Yuli, shugaban ma’aikatan gwamnatin ta nuna cewa kungiyoyi ma’aikata su na kawowa shirin karin albashin ma’aikata da gwamnati ta ke shirin yi cikas.

HoCS ta nuna cewa an nada wani kwamiti na musamman da zai duba maganar karin albashi bai-daya. Oyo-Ita ta ce a na cigaba da tattaunawa tsakanin kungiyoyin ma’aikata da gwamnatin kasar.

KU KARANTA: Majalisar Najeriya ta yi alkawarin hada karfi da karfe da Gwamnatin Buhari

Winifred Oyo-Ita ta ce shugaba Muhammadu Buhari a shirye ya ke da ya ga an fara biyan ma’aikata sabon mafi karancin albashi a fadin kasar nan, kuma a na ta yarjejeniya da ma’aikata.

Sai dai shugabar ma’aikatar ta ce: “Akwai wasu bukatu marasa bullewa da kungiyoyin ma’aikata ke kawowa. Domin gudun a cigaba da bata lokaci mu ka nemi a fara biyan albashin daga Afrilu.”

Misis Oyo-Ita ta bayyana cewa manufar soma biyan karin albashin daga Watan Afrilu kamar yadda Buhari ya bada umarni shi ne domin gujewa matsaloli daga ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel