Mayakan Boko Haram da suka tuba zasu iya zama shugaban kasa

Mayakan Boko Haram da suka tuba zasu iya zama shugaban kasa

Manjo Janar Abdulmalik Biu, kwamandan rundunar soji ta 7, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram da suka tuba, suka ajiye makansu, su na da damar zama shugaban kasa a Najeriya.

Biu ya bayyana hakan ne yayin kira ga mayakan kungiyar Boko Haram a kan su ajiye makamansu, su tuba, tun kafin rundunar soji ta rufe kofar karbar tuban 'yan kungiyar.

Ya bayyana hakan ne a gaban manema labarai yayin da ya ke ganawa da su.

A cewarsa, "mayakan kungiyar Boko Haram zasu iya ajiye makamansu, su koma cikin mutane su yi rayuwa kamar kowa. Dan Boko Haram da ya tuba zai iya amfanar rayuwarsa kamar ragowar mutane, kuma idan ya zama mutum nagari har shugaban kasa zai iya zama.

"Za su iya zama mutane masu amfani idan suka daina bata lokacinsu, suka ajiye makamansu. Shi yasa muke kira gare su da masu daukan nauyinsu da su yi amfani da damar da muka basu ta su tuba, su zubar da makamansu na yaki tun kafin lokaci ya kure musu."

DUBA WANNAN: Miliyan N8.5 da ake bamu duk wata ta yi mana kadan - Dan majalisa

Sannan ya cigaba da cewa, "abinda yafi musu alheri shine su ajiye makamansu. Zamu cigaba da yin kokari wajen tabbatar da zaman lafiya a matsayin mu na kwararru sojoji. Ba zamu bari zantukan wasu mutane su janye hanklinmu daga kan aikinmu ba.

"Najeriya na bukatar zaman lafiya, yankin arewa maso gabas na bukatar zaman lafiya, mutanen jihar Borno na son lafiya, domin sai da zaman lafiya ake samun cigaba, kuma hakan ne yasa muke cewa komai da lokacinsa. Idan mun shafe shekaru takwas muna yaki, yanzy lokaci ne na zaman lafiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel