Yan sanda sun kama mai kwarmato kan batan N232bn daga asusun Babban Bankin Najeriya

Yan sanda sun kama mai kwarmato kan batan N232bn daga asusun Babban Bankin Najeriya

-Yansanda sun kama mai kwarmato, George Uboh da laifin batanci ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.

-Takardar tuhumar, wadda SaharaReporters ta yada a shafinta na yanar gizo, an shigar da kara a Babbar Kotunan Birnin Tarayya, Abuja biyo bayan korafe-korafe akan Gwamnan na CBN akan almundahana da N232bn.

Yansanda sun kama mai kwarmato, George Uboh da laifin batanci ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.

Takardar tuhumar, wadda SaharaReporters ta yada a shafinta na yanar gizo, an shigar da kara a Babbar Kotunan Birnin Tarayya, Abuja biyo bayan korafe-korafe akan Gwamnan na CBN akan almundahana da N232bn.

Daya daga cikin tuhumomin da aka karanto, “kai George Ubom a ranar 12 ga watan Mayu, 2019, cikin ikon wannan kotu mai alfarma, ka bada bayanai wanda kana da masaniya cewa karya ce akan Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bankin Najeriya akan yin baba kere da N232 ($760) ribar canji na kudaden ketare da aka maida asusun tarayya a 2017, ka aikata laifin bata sunan Gwamnan Babban Bankin Najeriya saboda haka ka aikata lafi mai hukunci sashe 140(B) na kundin shari’a.

KARANTA WANNAN: Cikin shekaru 19, yan majalisa sun handami N2trn kuma babu abun kirkin da sukayi

Emefiele, a wani fai-fai da aka yada a watan mayu ana zargin shi da batar da N500bn. fai-fan wanda Saharareporters ta yada anji muryar Gwamnan Babban Bankin, da mataimakin shi Edward Adamu, da Daraktan kudi Dayo Arowosegbe tare da mai taimakama Gwamnan na musamman Emmanuel Ukeje suna tattauna yadda zasu rufe maganar batan N500bn kudin da suka sata suka sanya a wani kasuwanci da bai tafi dai-dai ba.

Wani fai-fan anji Gwamnan yana cewa bai kamata ma’aikatar kudi, da majalisar dokoki su san zance ba. Sannan an ware N2bn ma hukumar cin hanci da rashawa ba tare da wani dalili ba.

Tuni dai Babban Bankin ya karyata, cewa babu wasu kudi da suka bace daga asusunta.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel