Barayi sun yi wa 'yar sanda duka, sun yi mata tsirara a Abuja (Bidiyo)

Barayi sun yi wa 'yar sanda duka, sun yi mata tsirara a Abuja (Bidiyo)

CSP Nana Bature Garba, wata jami'a a rundunar 'yan sandan Najeriy, ta sha duka a wurin wasu barayi tare da yi mata tsirara a garin Abuja.

A wata hira da ta yi da sashen Hausa na BBC, Nana ta yi bayani dalla-dalla yadda ta kasance tsakanin jami'an 'yan sanda da barayin da suka yi mata wannan cin mutunci.

"Suna na Nana Bature Garba. Ina son baku labarin abinda ya faru da ni lokacin da na ke DPO a ofishin 'yan sanda da ke Mpape a Abuja.

" Lokacin da na je Mpape suna da wata ka'ida cewa ba ka isa ka shiga kasuwar Panteka ka kama wani ba, ko kuma a kwato kayan mutane da aka sace aka sayar a kasuwar ba. Na ce sam ban yarda da hakan ba, ya za a ce akwai wani wuri da ake aikata laifi da dan sanda ba zai shiga wurin ba, ni kam sai na shiga.

"Na tara 'yan sandan ofishina na ce mu je wannan wuri tare da su. Tun kafin mu je ma mutanen Mpape suka dinga zuwa suna ce min Hajiya a'a, kar ki je wannan wuri domin ba shiga, na ce ni kam sai na shiga, ba zan fasa ba.

"Ina kyautata zaton cewa kamar sun samu labarin muna shirin zuwa wurin ne, domin muna isa wurin sai kawai suka yi mana kawanya, suka kewaye mu gaba daya, suka sako mana karnuka. Ganin haka sai muka budewa karnukan wuta, ai kamar dama abinda suke jira kenan, kawai sai muka ji ruwan duwatsu da sanduna daga kowanne bangare suna sauka a jikinmu. A cikin duk 'yan sandan da muka tafi wajen mu 18 babu wanda bai ji ciwo ba.

"Sun yi mana duka ba na wasa ba, don ni kaina DPO saida suka yaga min kaki na, kai ba ma iya kaki kadai ba, hatta rigar mama da ke jikina saida aka yaga, sai wata mata ce ta zo ta bani zani na daura," a cewar CSP Nana.

DUBA WANNAN: Yadda aka kashe min miji a harin kyamar bakar fata a kasar Kyrgyzstan - Amina Aliyu

Nana ta kara da cewa sai waya suka yi hedikwatar 'yan sanda aka kawo musu agaji, amma kafin ma 'yan uwansu su karaso sun gama galabaita don ko tashi ya gagare su.

Ta cigaba da cewa, "aka samu dai Allah ya taimaka aka kawo mana agaji, aka kwashe mu aka tafi da mu."

Nana ta ce hakan bai sa ta hakura ba, domin bayan ta samu lafiya ta kara koma wa wurin saboda ta bi kwakwafin meye a wurin da basa son hukuma ta sani.

Sai dai, Nana ta canja salo, don ta ce sai da ta rubuta wa kwamishinan 'yan sandan Abuja wasika domin a yi taron dangi a sake koma wa wurin.

Nana ta ce a haka suka samu nasarar shiga wurin, kuma tun bayan wannan lokaci suka bude hanyar shiga kasuwar domin kamo masu laifi ko kwato kayan sata.

Kalli faifan bidiyon hira da CSP Nana a nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel