Yan sanda sun damke wata azzalumar mata da ta kusa makanta yarinya karama dake mata aiki

Yan sanda sun damke wata azzalumar mata da ta kusa makanta yarinya karama dake mata aiki

-Rundunar yan sanda ta jihar Ebonyi ta bayyana cewa tayi nasarar kama wata mata da ta ci zarafin yar aikinta inda ta yi mata rauni a ido

-Mai magana da yawun rundunar yan sanda, DSP Loveth Oda ta bayyana lamarin a matsayin cin zarafi da bautar da yara wanda haka ya sabawa dokar kasa

-Yarinyar ta bayyana ma manaima labarai cewa an dake ta ne saboda ta yi amfani da hodar wanki sa'annan uwar dakin ta gargade ta akan kada ta sake ta fadi gaskiyar abinda ya faru

Rundunar yan sanda ta jihar Ebonyi ta bayyana cewa tayi nasarar kama wata mata mai suna Nkechinyere Aja da tai ci zarafin yar aikin gidanta mai suna Chinonyerem Chiude inda ta yi mata rauni a ido.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda, DSP Loveth Oda ta bayyana lamarin a matsayin cin zarafi da bautar da yara wanda haka ya sabawa dokar kasa.

Odah ta bayyana cewa, mai laifin, wadda ma’aikaciyar asibitin Mile Four ce a Abakaliki, ta raunata yar aikin na ta a ido a lokacin da take dukanta saboda tayi amfani da hodar wanki a maimakon dunkulen sabulu wajen yin wanke wanken tukane.

Mai magana da yawun rundunar ta bayyana cewa an saki mai laifin bayan da aka kamata saboda ta je ta kula da lafiyar yar aikin tata da ta raunata.

KARANTA WANNAN: Tsohon gwamnan Zamfara, Abdul aziz Yari ya ce yin sulhu da yan ta'adda ba zai haifar da 'da mai ido ba

Yar aikin gida, wacce yarinya ce karama yar aji hudu a makarantar firamare ta New Era dake a Abakaliki ta bayyana ma manaima labarai cewa uwar dakin ta raunata ta a idonta na dama a lokacin da take bugunta. Ta bayyana cewa uwar dakin ta gargade ta akan kada ta sake ta fadi gaskiyar abinda ya faru.

Ta ce : “Antina ta fusata sosai bayan da na fada mata cewa nayi amfani da hodar wanki a maimakon dunkulen sabulu wajen wanke faranti, ta duke ni da bulala har sai da ta ji mani ciwo a ido na na dama.”

Shugabar makarantar New Era, Dorothy Magbo ta bayyana cewa ta kai maganar zuwa ga ministirin mata da inganta rayuwar al’umma bayan da uwar dakin yarinyar ta ki amsa gayyatar da ta yi mata.

Ta ce : “Na lura cewa Chiude na cikin damuwa, sai na tunkare ta, shine take fada mani cewa antinta ta duke ta saboda tayi amfani da hodar wanki wajen wanke faranti a maimakon dunkulen sabulu.”

Godwin Igwe, daraktan inganta rayuwar yara na ministirin, ya bayyana damuwarshi game da afkuwar lamarin inda ya kwatantashi da rashin sanin darajar ran dan adam.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel