An hurowa Buhari wuta ya fito da Ministoci a cikin makon nan kafin a tafi hutun Majalisa

An hurowa Buhari wuta ya fito da Ministoci a cikin makon nan kafin a tafi hutun Majalisa

Majalisar dattawa ta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari daga nan zuwa Ranar Juma’a mai zuwa ya aiko mata da sunayen wadanda ya ke so a tantance a matsayin Ministocinsa wannan karo.

Kamar yadda mu ka samu labari daga wata Jaridar kasar nan, idan har shugaban kasar bai mikawa majalisa jerin Ministoci a makon da za a shiga ba, Sanatocin kasar za su tafi dogon hutu.

A duk shekara ‘yan majalisar tarayya su kan tafi hutun shekara daga Ranar 26 ga Watan Yuli har sai zuwa 26 ga Satumba. Idan babu labarin nadin Ministoci, majalisar za ta tafi hutu kwanan nan.

Sanata Adedayo Adeyeye wanda shi ne shugaban kwamitin harkokin watsa labarai a majalisar, ya bayyana cewa za su tafi hutun shekarar a makon gobe muddin ba a aiko da sunayen Ministoci ba.

KU KARANTA: An fara kishin-kishin din lokacin da Buhari zai nada Ministoci

Adedayo Adeyeye ya ke cewa majalisar dattawa ba ta sa wa shugaban kasar takamaimen lokaci da a ka kayyade domin ya turo da sunayen wadanda ya ke so ya nada a matsayin Ministocinsa ba.

Sanata Adeyeye ya ke cewa a duk lokacin da shugaba Buhari ya ga dama, zai iya turawa majalisa jerin sababbin Ministocin kasar, kuma har za su iya dakatar da hutun na su domin cigaban kasa.

Mai magana da yawun majalisar ya nuna cewa za su matsawa shugaba Muhammadu Buhari ya fito da sunayen Ministocin domin kuwa wannan ne kurum aikin da zai iya rike su yanzu a ofis.

Shi ma shugaban marasa rinjaye a majalisar, Enyinnaya Abaribe, ya tabbatar da cewa Sanatoci za su tafi hutu a lokacin da a ka yanke, har ya na ganin babu abin da zai sa su fasa wannan hutun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel