Yanzu-yanzu: Mutum hudu sun mutu bayan gini ya rufto musu a Delta

Yanzu-yanzu: Mutum hudu sun mutu bayan gini ya rufto musu a Delta

A kalla mutane hudu ne suka rasu sakamakon ruftowar wani gini mai hawa uku da ke kan ginawa a garin Abraka da ke karamar hukumar Ethiope Ta Gabas na Jihar Delta.

An kuma ruwaito cewar akwai wasu mutane da suka makale a cikin ginin da ya rufto.

A garin Abraka ne Jami'ar Jihar Delta ta ke.

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

Duk da cewar ba a tabbatar da ainihin dalilin da ya janyo ruftawar ginin ba, an gano cewa ginin ya rufta ne yayin da ake ruwa kamar da bakin kwarya a safiyar ranar Asabar kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Wata majiya ta ce wadanda ginin ya ruftowa leburori ne da sauran ma'aikata da suka fake cikin ginin suna jirar ruwan saman ya tsaya su koma aiki amma kwatsam sai wani bangare na ginin ya rufta.

Mutanen da ke aikin ba su da yawa sosai amma an tabbatar da rasuwar mutane hudu a cikinsu.

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel