Kashim Shettima ya nemi Majalisa ta gyara harkar ilmin Boko a Najeriya

Kashim Shettima ya nemi Majalisa ta gyara harkar ilmin Boko a Najeriya

Mun samu labari cewa a na ta magana a kan tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, wanda yanzu Sanata ne a karkashin jam’iyyar APC, bayan wasu maganganu da ya yi kwanan nan.

Sabon Sanatan na APC ya nemi ‘yanuwansa da ke majalisar tarayya da su dage wajen ceto harkar ilmi daga tabarbarewa a Najeriya. Kashim Shettima ya koka da halin da ilmi ya shiga a kasar.

Sanatan ya nuna cewa idan a ka yi sake, a ka yi wa harkar ilmi rikon sakainar kashi a kasar nan, lallai kowa zai dawo ya na kuka da kan sa; daga manya har Talakawa marasa kudi inji Shettima.

Kashim Shettima da ya ke magana a zauren majalisa ya ce tabarbarewar ilmi zai jawo abin da zai ci mutanen kasar nan domin a haka ne a ke samun wadanda su ke burmawa cikin aikin assha.

KU KARANTA: Lawan ya yi abin da Saraki ya gazawa yi wa Shugaba Buhari a Majalisa

‘Dan majalisar ya kara da cewa mafi yawan su da su ka zama wasu a yau, sun yi karatu ne a makarantun gwamnati, wanda yanzu sun kama hanyar ratattakewa saboda sakacin hukuma.

Tsohon gwamnan ya ke cewa Duniya ba za ta yi wa ‘yanuwansa da ke majalisa dadi ba, muddin ba a kama hanyar dawo da martabar wannan makarantu da a ka sani da daraja a zamanin da ba.

‘Dan majalisar mai wakiltar Borno ta tsakiya ya ke cewa a sauran kasashe an yi nisa da batun manyan fasaha, inda a ke kirkirar mutum-mutumi, amma Najeriya ta na wani halin baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel