A jajirce nake wajen tsiratar da Najeriya - Buhari

A jajirce nake wajen tsiratar da Najeriya - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 19 ga watan Yuli, ya bayyana cewa har yanzu yana kan jajircewa domin tsiratar da Najeriya.

Kasar dai ta dade tana fuskantar babban matsala guda akan rashin tsaro, wanda yayi sanadiyar da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya saki wata budaddiyar waka zuwa ga shugaba Buhari a ranar Litinin, inda ya soki gwamnatinsa.

Amma da yake Magana a adar Shugaban kasa lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar magoya bayan Buhari/Osinbajo karkashin jagorancin Shugaban kungiyar, Usman Ibrahim, Buhari yace manufar shine son ganin Najeriya ina Iyalai za su kasance cikin tsira sannan yara su samu damar yin rayuwa mai inganci.

“A matsayinku na shugabanni a garuruanku daban-daban, ina bukatarku da ku isar da sakon zuwa garuruwanku. Ba batun siyasa, addini ko kabilanci bane. Akan samar da Najriya inda iyalinmu za su kasance cikin tsira sannan yaranmu su samu dama mai yawa domin yin rayuwa mai inganci,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnonin kudu maso yamma sun caccaki kiran da aka yiwa makiyaya na su koma arewa

Da yake godiya ga kungiyar akan kokarinta da jajircewarta a lokacin kamfen din zaben 2019, ya bayyana cewa gwamnatisa ta jajirce wajen sauke hakokinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel