Na yi wa 'yar ciki na fyade ne domin bata kariya - Mahaifi

Na yi wa 'yar ciki na fyade ne domin bata kariya - Mahaifi

Wata kotun Majistare da ke zamanta a Iwo Road a garin Ibadan, a ranar Alhamis ta bayar da umurnin bawa wani mai gadi dan shekaru 37, Wasiu Orilonise masauki a gidan yarin Agodi bayan ya amsa cewa ya yi wa diyarsa mai shekaru 15 fyade domin ya kare ta.

An gurfanar da wanda ake zargin ne bisa tuhumarsa da aikata laifi daya na saduwa da 'yar cikinsa.

Mai shigar da karar, Mista Sunday Ogunremi ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargin a Disamban 2018 a kauyen Omo da ke Agbofieti da ke Ibadan ya yi wa wata Orilonise Adenike fyade.

DUBA WANNAN: Buhari ya canja hotonsa da ake amfani da shi a hukumance

Ogunremi ya ce laifin ya sabawa sashi na 34 da kananan sashi na 1 da 2 na dokar kare hakkin yara na jihar Oyo ta shekarar 2006.

Orilonise ya shaidawa kotu cewa shi ne ya ke kulawa da Adenike da sauran 'yan uwanta tun bayan rasuwar matarsa a shekarun da suka gabata.

Ya kuma shaidawa da kotun cewa ya aikata fyaden ne domin ya kare diyarsa.

Orinlonise ya ce lamarin ya faru ne yayin da ya ke kokarin dubawa ko diyarsa tana nan da budurcinta, kuma bayan ya gano cewa tana tare da budurcin ta sai ya fara saduwa da ita duk safe kafin ta tafi makaranta da kuma dare kafin tayi barci.

Alkalin kotun ta gargadi iyaye maza da ke saduwa da 'ya'yan su da sauran yara kananan inda ya ce suna bari shaidan yana amfani da su wurin lalata tarbiyyan al'umma.

Ya bayar da umurin a cigaba da rike wanda ake zargin a gidan yarin Agodi yayin da ya ke jirar shawarar kwararru daga ofishin sauraron karrakin al'umma (DPP).

Ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 30 ga watan Yulin 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel