Majalisa sun tantance Aliyu Abubakar a matsayin Kwamishinan NCC

Majalisa sun tantance Aliyu Abubakar a matsayin Kwamishinan NCC

Idan ba ku manta ba a 2016, shugaban kasa Muhammadu Buharu ya tabo aiko sunayen wadanda za a nada a matsayin Kwamishinonin hukumar NCC mai kula da harkar sadarwa a Najeriya.

Sai dai ‘yan majalisa a wancan lokaci na mulkin Bukola Saraki, sun yi watsi da sunan wani daga cikin wadanda shugaban kasar ya nemi ya ba wannan mukami watau Aliyu Saidu Abubakar.

An yi dace yanzu ‘yan majalisar tarayyar sun amince da Alhaji Aliyu Saidu Abubakar a matsayin Kwamishina maras ikon zartarwa da ke wakiltar yankin Arewa maso Gabas Hukumar NCC.

KU KARANTA: Wasu Gwamnoni sun gaza nada Kwamishinoni bayan makonni da hawa mulki

Bayan Aliyu Abubakar, Sanatocin sun amince da wasu nade-naden da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi. Daga cikin su akwai Injiniya Uba Maska wanda zai wakilci Arewa ta Yamma.

Haka zalika an sake sabunta mukaman Farfesa Millionaire Abowei a matsayin Darekta mai wakiltar Kudu maso Kudu da kuma Abdulazeez Mohammed Salman daga shiyyar Arewa ta tsakiya.

A wancan majalisa ta takwas, an yi ta samun ta-ta-bur-za tsakanin fadar shugaban kasa da kuma majalisar dattawan kasar da Bukola Saraki ya jagoranta. A karshe Saraki ya rasa zabe da kujerarsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel