Dalilin da ya sa NFF ba za ta yi gigin-gigin tsige Gernot Rohr ba

Dalilin da ya sa NFF ba za ta yi gigin-gigin tsige Gernot Rohr ba

Yayin da a ke shirin kammala gasar AFCON na Afrika, bayanai sun bayyana game da abin da ya sa Gernot Rohr zai cigaba da zama a matsayin babban kocin kungiyar Super Eagles na Najeriya.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya watau NFF ta bayyana cewa babu maganar sallamar Gernot Rohr daga matsayin da ya ke na mai horas da ‘yan wasan kwallon kafan kasar a wannan lokaci.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Sports Extra, NFF ta yi watsi da kiran da wasu ke yi na sauke Gernot Rohr bayan da Najeriya ta gaza lashe Gasar cin kofin AFCON na Nahiyar Afrika.

Bajamusen kocin na Super Eagles ya na da ragowar shekara guda a kwantiragin da ya sa hannu da Najeriya, kuma dole a biya shi kudi har Dala miliyan 1 idan a ka sabawa wannan yarjejeniya.

KU KARANTA: Najeriya ta doke Tunisiya a gurbin zama na uku a Afrika

Da zarar NFF ta raba gari da Koci Gernot Rohr, za ta biya Mai horas da ‘yan wasan na ta kudin da su ka haura Naira miliyan 300. Wannan ya sa ya zama dole a jira wa’adin babban Kocin ya cika.

Amaju Pinnick wanda ke jagorantar kungiyar NFF ta Najeriya ya fito ya bayyana cewa ba za su sallami Kocin mai shekaru 66 ba. Pinnick ya ce Rohr ya cika sharudan da a ka gindaya masa.

Bayan samun wannan labari ne, Gernot Rohr ya samu taimakawa Najeriya wajen lashe matsayin na uku a Gasar AFCON na bana. Haka zalika ‘Dan wasan Najeriya ya tashi da kwallaye 5 a Gasar.

NFF ta ce dama an yi da Kocin na Super Eagles cewa Najeriya za ta kai matsayin gaf da karshe ne a wasan cin kofin Afrika. Yanzu dai Rohr ya yi nasara a wasani 20 cikin 35 da ya buga da kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel