Yanzu Yanzu: Ku yi watsi da kiran kungiyar dattawan arewa na barin kudancin kasar – Buhari ga makiyaya

Yanzu Yanzu: Ku yi watsi da kiran kungiyar dattawan arewa na barin kudancin kasar – Buhari ga makiyaya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dukkanin yan Najeriya da su yi watsi da kiran da kungiyar dattawan arewa tayi kwanan nan zuwa ga Fulani makiyaya, inda ta bukaci da su bar yankin kudancin Najeriya.

Shugaba Buhari a wani jawabi dauke das a hannun babban mai bashi shawara na musamman a harkokin labarai, Mallam Garba Shehu a Abuja yace, “Dukkanin al’umman Najeriya na da yancin yawo da zama a kowani yanki na kasar da suke muradi, imma su kasance yan asalin yankin ko akasin haka.

“Kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasar, gwamnatin Najeriya kuma gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kare al’umman kasar a duk inda suka tsinci kansu.

“Babu wanda ke da yancin cewa wata kungiya ko wani mutum ya bar wani yanki na kasar, imma arewa, kudu, yamma ko gabas."

Shugaban kasar ya nemi sanin kudirin kungiyar dattawan arewa da sauran shugabanni da ke shiga lamarin tare da shawarar da bai dace ba.

KU KARANTA KUMA: Fulani suna da 'yancin zama a kowanne yanki na Najeriya - Yakasai

Yace: “Ba su da ikon yin irin wannan sanarwar.”

Buhari yayi kira ga dukkanin yan Najeriya da su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel