Kai tsaye: Najeriya - 1, Tunisia 0 (Neman na uku)

Kai tsaye: Najeriya - 1, Tunisia 0 (Neman na uku)

A ranar Laraba ne ake buga neman na uku tsakanin Najeriya da kasar Tunisia a gasar cin kofi nahiyar Afrika da ake bugawa a kasar Masar (Egypt).

Najeriya ta fito da 'yan wasanta kamar haka:

Kai tsaye: Najeriya - 1, Tunisia 0 (Neman na uku)

Kai tsaye: Najeriya - 1, Tunisia 0 (Neman na uku)
Source: Facebook

Najeriya ta fito da dukkan 'yan wasanta da ta saba fitowa da su in banda gabatar da Ola Aina, wanda ya maye gurbin Chigozie Awaziem da Francis Uzoho wanda ya maye gurbin Daniel Akpeyi.

An take wasa da misalin karfe 8:00 na dare.

Dan wasan gaba na Najeriya, Odion Ighalo, ya zira wa Najeriya kwallo ta farko a minti na uku da fara buga wasa.

An tafi hutun rabin lokaci, Najeriya ce a gaba da kwallo daya mai ban haushi da ta saka a ragar Tunisia.

Victor Osimhen ya canji Ighalo a yayin da aka dawo daga hutun rabin lokaci a filin wasa na Al Salam, in da za a sake shafe wasu mintuna 45 ana fafata wa tsakanin Najeriya da kasar Tunisia.

An bawa mintuna 70 baya, har yanzu Najeriya na da kwallo 1, yayin da Tunisia ke nema.

An cire Ahmed Musa, an sako Moses Simon a daidai minti na 75.

Najeriya ta yi canji na karshe, Samuel Kalu ya canji Chukwueze a minti na 90.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Za ka iya aiko mana da labari ta hanyar cike wanna fom da ke kasa:

https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSch6m8qBDJY3fmT8OH0Dy7Sqkrvwt-tveaPURetOsKjYb_4cQ/viewform

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel