Hukumar kwastam ta kama motar asibiti cike da katan-katan na kwayar Tramadol

Hukumar kwastam ta kama motar asibiti cike da katan-katan na kwayar Tramadol

-Hukumar kwastam ta kama motar ambulas dauke da katan goma na kwayar Tramadol a Legas

-Konturolan hukumar fasa qwarin na shiyyar Apapa dake Legas ne ya bada wannan labarin ga 'yan jarida inda ya ce a daren ranar Juma'a ne aka kama motar

-Abinda har yanzu ba'a samu ba shi ne ragowar katan 211 da sukayi sama ko kasa

Hukumar fasa qwarin Najeriya ta kwastam reshen jihar Legas ta damke wata motar ambulas dauke da katan goma na kwayar Tramadol.

Hukumar ta bayyana ma jaridar Leadership cewa anyi kiyasin kudin kwayar zai kai naira miliyan uku, kuma an dauko kwayar ne daga wata katafariyar kwantena dake tashar jiragen ruwan Apapa.

KU KARANTA:Gwamnatin Zamfara za ta dauki matasa 3,800 aiki

An kama wannan motar ambulas din mai lamba LND 605 XW a cikin tashar Apapa dauke da abinda ba a tabbatar da ko meye shi ba.

Bayan an kama wannan motar ne bincike ya yi sanadiyar gano wata katafariyar kwantena wadda ke dauke da katan 211 na kwayar amma sai dai kuma an nemesu an rasa.

Konturolan hukumar mai kula da shiyyar Apapa, Muhammad Abba Kura ya ce da misalin karfe 11 na dare Juma’a ne a ka kama motar.

Konturolan ya ce: “ Kwantenar ta kasance daya daga cikin wadanda aka shigo da su qasar nan ta jirgin ruwa, amma sai dai mun fahimci cewa an balle ainihin marfin kwantenar an sauya da wani na daban.”

Akwai ma’aikatan Medbury Medical Services dake hannun hukumar kwastam kasancewar sune ‘yan rakiyar motar da aka samu dauke da kwayoyin.

Kura ya sake cewa: “ Muna cigaba da gudanar da bincike domin kamo duk mutanen dake da sa hannu cikin shigowa da wadannan kwayoyin Najeriya da kuma neman sauran katan 211 da su kayi sama ko kasa.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel