Akasi: kuskuren rubutu ya zaunar da wani mutumi a Kurkuku tsawon shekaru 14

Akasi: kuskuren rubutu ya zaunar da wani mutumi a Kurkuku tsawon shekaru 14

Allah Sarki, tsautsayi baya wuce ranarsa, wani mutumi mai shekaru 48 ya bada labarin yadda kuskuren rubutu ya zaunar dashi a gidan yari tsawon shekaru 14 a Najeriya, har sai a shekarar 2019 aka gyara wannan matsala, aka sako shi.

Wannan mutumi mai suna Derrick Addai dan asalin jahar Cross Rivers ne, ya bayyana cewa a shekarar 2000 aka kamashi da laifin safarar kwayoyi a kasar Thailand tare da wasu mutane 30, inda aka yanke musu hukuncin zaman kurkuku.

KU KARANTA: Daukan aiki: Rundunar sojan ruwa ta saki sunayen yan Najeriyan da suka cancanci shiga aikin Soja

Bayan sun kwashe shekaru 5, daga bisani tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya sanya baki cikin lamarinsu, kasar Thailand ta mikasu ga Najeriya, kai tsaye aka zarce dasu kurkukun jahar Ogun, bayan wasu yan watanni kuma Obasanjo ya yi musu afuwa.

Sai dai ba anan gizo ke sakar ba, saboda da aka kawo sunayen wadanda aka yi ma afuwan, sai aka baiwa Derrick ya bude takardar ya karanto sunayen, sai dai kash! Babu sunansa a ciki, kuma ga adadin sunayen nan 30 ya cika cif cif, ashe sunan wani ne aka maimaita sau biyu, aka fidda sunan Derrick bisa kuskure.

Nan da nan aka saki sauran mutane 29, shi kuma Derrick aka bashi hakuri ya cigaba da zama a Kurkukun har sai an gyara wannan matsala daga fadar shugaban kasa, shima marubucin da ya yi wancan rubutu da yaga takardar sai ya musanta rubutata wai don ya kare aikinsa, yace a bashi kwana biyu zai gyara, shikenan ya manta da batun gaba daya.

Gyara yau ne, gyara gobe ne, a haka har Derrick ya zauna shekaru 14 a Kurkukun jahar Ogun sai a shekarar 2019 da Sarkin Oke-Ona Oba Adedapo Tejuoso da kuma daraktan cibiyar tallafa ma mazauna gidan yari, Bishop Kayode Williams suka shiga maganar, har suka samu nasarar fiddashi.

Ikon Allah, Allah kada ka hadamu da jarabawar da ba zamu iya ci ba, Amin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel