Yadda mara lafiya ya kashe kansa da gilashin taga a asibitin UBTH

Yadda mara lafiya ya kashe kansa da gilashin taga a asibitin UBTH

Rahotanni sun bayyana cewa wani mara lafiya ya kashe kansa Asibitin Koyarwa na Jami'ar Benin a cewar mai magana da yawun asibitin Mista Joshua Uwaila.

Lamarin ya faru ne a sashin dakin kwantar da masu hatsari na asibitin a daren ranar Asabar.

Anyi ikirarin cewa mai jinyan ya kashe kansa ne yayin da ya ke jiran likita.

Mara lafiyan da ba a bayyana sunansa ba ya caka wa kansa kwalba ne da ya ciro daga tagar da ke kusa da gidansa.

DUBA WANNAN: Shaidan PDP ya bayyana abinda mahaifinsa ya fada masa a kan asalin Atiku

Matar mara lafiyar ta fita domin ta sayo wani abu a wani shago da ke cikin harabar asibitin yayin da mummunan lamarin ya faru, inji wani da abin ya faru a idonsa.

Wani shaidan da ya nemi a boye sunansa, wanda shima mai jinya ne a asibitin ya ce mamacin ya zo asibitin ne tare da matarsa.

"Kwatsam kawai ya rikice ya karya kwalba da ke tagar da ke kusa da tagansa kuma ya caka wa wuka," inji shi.

"Matarsa ta fita. Ta fita waje ta siyo wani abu. Duk jini ya zuba a ko ina. Munyi sa'a bamu samu rauni ba," inji wanda ya bayar da shaidan.

Daga bisani an tafi da gawar mammacin zuwa dakin ajiye gawarwaki na asibitin.

A yayin da ya ke tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar Talata a Benin, mai magana da yawun asibitin ya ce abin bakin ciki ne.

"Wani matashi da aka kwantar a asibitin mu da ba za a iya bayyana abinda ke damunsa ba saboda sirri ne ya fasa kwalban taga ya caka wa kansa," inji shi.

Uwaila ya ce anyi kokarin ceto rayuwarsa amma hakan bai yi wu ba.

"A halin yanzu ana sauraron sakamakon abinda ya kashe shi," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel