Hukumar NFF za ta cigaba da aiki da Gernot Rohr da da sallamar Najeriya daga AFCON

Hukumar NFF za ta cigaba da aiki da Gernot Rohr da da sallamar Najeriya daga AFCON

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick ya musanta rade radin da ke yadawa na cewa wai zasu sallami mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Gernot Rohr.

Pinnick ya bayyana haka ne a ranar Talata, 16 ga watan Yuli yayin da yake ganawa da yan jaridu a kasar Cairo, inda yace duk da cewa sun amince akwai kurakuran da Rohr ya tafka, amma zasu kyaleshi da kungiyar don ya gyara kurakuransa.

KU KARANTA: Jerin kamfanoni 34 da gwamnati ta baiwa kwangilar hakar danyen man fetir a Najeriya

Akwai mabambamta ra’ayoyi da dama a tsakanin yan Najeriya, inda wasu ke ganin Rohr yana kan turbatr dawo da martabar kungiyar Super Eagles, yayin da wasu kuma ke ganin Rohr bai tabuka wani abin azo a gani ba.

“Za mu kyaleshi ya cigaba da aikinsa, ina da yakini mai kyau game da shi. Rohr ya kaimu zuwa wasan zagaye na kusa da na karshe, kuma shine yarjejeniyar da muka yi da shi, don haka ya cika alkawarin daya daukan mana.

“A yanzu muna da wasan neman matsayi na uku tsakaninmu da Tunisia, kuma muna da yakinin Najeriya ba za ta koma gida ba sai ta samu wani dan martaba ko yaya. Na san akwai masu kira mu sallami Rohr, amma ba zamu yi hakan ba.

“Asali ma Rohr zai tafi kungiyar Bayern Munich don kara samun horo bayan kammala gasar AFCON, muna da dogon tsare tsare da muke son cimmawa tare dashi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel