An gano babban soja da ke shirya yi wa shugaban kasa juyin mulki

An gano babban soja da ke shirya yi wa shugaban kasa juyin mulki

- Amai Auxillia Mnangagwa, uwargidan shugaban kasar Zimbabwe ta yi zargin cewa wani soja na yi mata leken asiri tare da shirin yi wa mijinta juyin mulki

- Wani dan asalin kasar Zimbabwe ne ya fara tona asirin sojan da uwargidan shugaban kasar ke korafin cewa ya na shirin yi wa mijinta juyin mulki

- Babban hafsan sojin, laftanal kanal Samson Murombo, kwamanda ne a rundunar sojoji ta 1 da ke tsaron shugaban kasa

An gano babban sojan kasar Zimbabwe da ke yi wa Amai Auxillia Mnangagwa, uwargidan shugaban kasar Zimbabwe leken asiri tare da shirin kifar da gwamnatin shugaba Emerson Mnangagwa.

Babban hafsan sojin, laftanal kanal Samson Murombo, kwamanda ne a rundunar sojoji da 1 da ke tsaron shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Banyankole: Kabilar da kanwar uwar amarya ke kwana da ango domin tabbatar da kwazonsa

Wani dan kasar Zimbabwe ne ya fara tona asirin kanal Murombo a shafinsa na Tuwita kafin daga bisani tsohon ministan ilimi a kasar, Jonathan Moyo, ya yada wani faifan sautin muryar matar shugaban kasa, Auxillia Mnangagwa, ta na babatu a kan shirin wani soja na yi wa mijinta, shugaba Emmerson Mnangagwa, juyin mulki.

Kazalika ta koka a kan yadda sojan ke yi mata leken aisiri.

Ana zargin kanal Murombo da hada baki da da Mhlanga da Manjoro domin yi wa Mnangagwa juyin mulki, kamar yadda uwargidan shugaban kasa ta yi zargi.

An gano babban soja da ke shirya yi wa shugaban kasa juyin mulki

Kanal Morumbo
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel