Buhari yana ganawa da tawagar NMA a fadar Aso Rock

Buhari yana ganawa da tawagar NMA a fadar Aso Rock

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya gana da mambobin kungiyar likitoci na kasa wato Nigerian Medical Association (NMA).

An fara ganawar ne misalin karfe 11.30 na safe a ofishin shugaban kasar da ke fadarsa a birnin tarayya, Abuja.

Wata babbar mota kirar coaster ce ta kai mambobin kwamitin na NMA gidan gwamnatin misalin karfe 11.07 na safe.

Kwamitin wadda wa'addin ta ya fara daga 2018 kuma zai kare a 2020 ta kaiwa shugaban kasar irin wannan ziyar a watan Yulin 2018.

Shugaban kwamitin na NOC, Dakta Francis Adedayo Faduyile shine shugaban NMA.

DUBA WANNAN: Fashi da makami: Jerin sunayen sojoji 5 da ake nema ruwa a jallo

Mambobin kwamitin sun hada da shugaban, Dr. Kenneth Mingeh Tijo, mataimakin shugaba, Dr. Ofem Egbe Enang, Sakatare, Dr. Olumuyiwa Peter Odusote.

Saura sun hada da mataimakin sakatare, Dr. Benjamin Ikechukwu Umezurike, Ma'aji na Kasa, Dr. Ayuwaja Nayagawa, Sakatern Kudi na Kasa, Dr. Abdulgafar O. Jimoh, Jami'in hulda da Jama'a, Dr. Obitade Sunday Obimakinde.

An kafa NMA ne domin taimakawa gwamnatin da al'ummar Najeriya wurin samar da ingantattun hanyoyin kula da kiwon lafiya a kasar.

Har ila yau, kungiyar tana aiki wurin kyautata alaka da walwala na likitoci a kasar.

Shugaban kasar yana bai kammala ganawar da ya ke yi yi da kungiyar ba a lokacin rubuta wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel