'Yan bindiga sun sace darektan ma'aikatar kasafin kudin jihar Zamfara

'Yan bindiga sun sace darektan ma'aikatar kasafin kudin jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da sace darektan ma'aikatar kasafin kudin jihar, Alhaji Hamza Salihu.

Yusuf Idris, babban darektan yada labaran gwamna jihar Zamfara, Bello Matawalle, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Litinin a Gusau.

"Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Bello Matawalle, ya bayyana damuwarsa bisa sace darektan ma'aikatar kasafi, Alhaji Hamza Salihu, wanda 'yan bindiga suka yi awon gaba da shi da wasu mutane biyu da ke tare da shi a Kachia da ke jihar Kaduna yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani aiki a jihar Nasarawa.

"Faruwar hakan babban abin takaici ne, musamman a daidai lokacin da ake kokarin kawo karshen garkuwa da mutane, satar shanu da sauran miyagun laifuka. Hakan ya nuna cewa wasu daga cikin masu aikata wadannan miyagun laifuka ba zasu tuba ba, ba tare da an zubar da jini ba," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Banyankole: Kabilar da kanwar uwar amarya ke kwana da ango domin tabbatar da kwazonsa

Kazalika, gwamnan ya nuna bakin cikinsa bisa kisan mataimakin darektan ma'aikatar kasafin Alhaji Kabiru Ismail, wanda 'yan bindigar suka kashe kafin su yi garkuwa da darektan da ragowar mutanen.

'Yan bindigar sun harbi wata mata da ke cikin motar sannan sun barta cikin jini a wurin da suka yi garkuwa da darektan da ragowar mutanen.

Gwamna Matawalle ya yi alkawarin hada kai da takwaransa na jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, da sauran hukumomin tsaro domin bankado 'yan bindigar da kubutar da mutanen da suka yi garkuwa da su.

Gwamnan ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin marigayi, Kabiru Ismail, tare da yin addu'ar Allah ya bawa iyalin hakurin jure rashinsa. (NAN)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel