2019: Atiku ya hana Lauyoyin Buhari bidiyoyin zabe a zaman kotu

2019: Atiku ya hana Lauyoyin Buhari bidiyoyin zabe a zaman kotu

A yayin da ake zaman shari’ar sauraron karar zaben shugaban kasa na 2019, an samu wata takaddama tsakanin Lauyoyin ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar da Lauyoyin shugaba Buhari.

Lauyoyin da su ka shigarwa Atiku Abubakar da kara a gaban kuliya sun gabatar da hujjoji a wasu tarin bidiyoyi bayan da su ka shigo kotu da tafkeken talabijin da kuma na’urar gafaka kirar Mac.

Gabatar da hujjojin Atiku Abubakar ke da wuya, sai Lauyan da ke kare shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi a mika masa fai-fen wannan bidiyo amma Lauyoyin PDP su ka ki.

Wani daga cikin tawagar Lauyoyin ‘dan takarar PDP ya yi wuf ya kashe talabijin da a ka haska bidiyoyin da Atiku Abubakar ya kafa hujja da su. Wannan ya jawo surutu a cikin zauren kotun.

KU KARANTA: Atiku ya gabatar da bidiyoyin da ke tabbatar da nasararsa a zaben 2019

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Lauyan na Atiku ya fadawa Chris Uche ya hana Lauyan shugaba Muhammadu Buhari, Alex Izinyon taba faifen ne da nufin gudun gurbata masa na’ura.

Babban Lauya Alex Izinyon ya yi mamakin yadda Takwaran na sa mai kare PDP zai hana shi amfani da faifen bidiyon. Wannan ya sa Alkali mai shari’a ya shiga cikin sa-in-sar Lauyoyin.

Masu kare Atiku na PDP din a gaban kuliya sun nuna cewa daga cikin dalilan da ya sa su ka hana kowa taba bidiyoyin shi ne hukuma ba ta tantance su ba tukuna kamar yadda doka ta ce.

Mai shari’a Mohammed Garba ya ja hankalin Lauyoyin su yi aikinsu cikin natsuwa ba tare da rikici ba. Alkalin ya ce bai dace shari’a ta zama abin rigima ba, bayan nan ya dakatar da shari’ar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel