Ba Buhari ne ke juya jami'an tsaron Najeriya ba - Ezekwesili

Ba Buhari ne ke juya jami'an tsaron Najeriya ba - Ezekwesili

- Tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili, ta ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba shine ke da iko da jami'an tsaron Najeriya ba

- Ezekwesili, tsohuwar 'yar takarar shugabar kasa, ta ce ba zai yiwu a cigaba da zama da shugaban kasa da ke zaune cikin kwanciyar hankali a fadarsa ba yayinda talakawa ke fuskantar kaubale ba

- Tsohuwar ministar ta ce kamata ya yi shugaban kasa ya bawa zaman lafiya fifiko fiye da komai

Tsohuwar ministar ilimi kuma tsohuwar 'yar takarar shugaban kasa, Oby Ezekwesili, ta ce lokaci ya yi da ya kamata shugaba Buhari ya karbi ragamar iko da jami'an tsaron kasar nan.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa tsohuwar ministar ta bayyana hakan ne yayin wata hira da ta yi da manema labarai a wurin taron gabatar da lakca, karo na 11, da cibiyar Wole Soyinka ta gudanar ranar Asabar a jihar Legas.

Legit.ng ta fahimci cewa Ezekwesili na wadannan kalamai ne a matsayin martani ga kisan Olufunke Olakunrin, diyar shugaban kungiyar 'yan kabilar Yoruba (Afenifere), Dattijo Reuben Fasoranti.

Ta ce Najeriya ba za ta cigaba da zama da shugaban kasar da ke zaune cikin kwanciyar hankali a ofis da fadarsa ba yayin da 'yan kasarsa ke fuskantar kalubale ba.

"Shugaban kasa ne babban jami'in tsaro kuma babban kwamandan rundunar tsaro ta kasa. Hanya mafi sauki da za a gane kwazon shugaba shine a kalli halin da tsaron kasa ke ciki. Idan tsaron kasa na tabarbarewa, alama ce da ke nuna gazawar shugaba da rashin damuwarsa da halin da 'yan kasarsa ke ciki.

"Ni ba na magana mai harshen damo, kai tsaye nake maganganu na. Ba zamu cigaba da zama da shugaban kasa da ke zaune cikin kwanciyar hankali a ofis da fadarsa ba, ba tare da damuwa da irin kalubalen da 'yan kasarsa ke fuskanta ba," a cewar Ezekwesili.

Sannan ta ci gaba da cewa, "ba ka sarrafa rundunar tsaron Najeriya ta hanayar da ya kamata. Tabbatar da tsaron 'yan kasa ne ya fi kamata ka bawa muhimmanci fiye da komai domin yin hakan gaba ya ke da duk wani mutunci da za a ce kana da shi a gwamnati."

Asali: Legit.ng

Online view pixel