Miyagu sun sake sace Mahaifiyar Koci Siasia a cikin Jihar Bayelsa

Miyagu sun sake sace Mahaifiyar Koci Siasia a cikin Jihar Bayelsa

Yanzu nan labari ya ke shigo mana cewa an sace Mahaifiyar tsohon kocin Super Eagles na Najeriya watau Samson Siasia. Wannan abu ya faru ne a cikin tsakar daren Ranar Litinin dinnan.

Kawo yanzu babu wanda ya san halin da wannan Baiwar Allah ta ke ciki. Labarin awon gaba da wannan tsohuwa ya zo mana ne daga Manema labarai a yau 15 ga Watan Yuni, 2019, da sassafe.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, wasu ‘yan bindiga sun shiga har gidan wannan mata ne da ke Garin Adoni a cikin karamar hukumar Sagbama da ke jihar Bayelsa sun yi awon gaba da ita.

An sace Misis Ogere Siasia ne da kimamin karfe 2 na tsakar dare a lokacin da jama’a ke sharar barci. Har yanzu dai jami’an tsaron kasar ba su yi magana game da wannan lamari ba tukuna.

KU KARANTA: An tsinci gawar wata Kwamishinar jihar Bayelsa a gida

Wannan ne karo na biyu da aka sace Ogere Siasia a cikin shekaru 4. Idan ba ku manta ba cikin Watan Satumban 2015, an taba sace Dattijuwar a gidanta, har ta yi kusan makonni 2 a tsare.

Wata majiyar ta bayyana cewa an yi yunkurin tuntubar jami’in da ke kula da harkokin yada labarai na ‘yan sandan jihar Bayelsa, Butswat Asinim, amma bai iya cewa komai ba kawo yanzu.

Samson Siasia ya bugawa Super Eagles kwallo a lokacin yana Matashi, sannan kuma ya horas da kasar a mataki da dama kuma a lokuta dabam-dabam wanda har a 2016 ya sake zama kocin ta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel