Najeriya su na cikin wadanda za su iya lashe Gasar AFCON – Riyad Mahrez

Najeriya su na cikin wadanda za su iya lashe Gasar AFCON – Riyad Mahrez

Mun ji Riyad Mahrez mai rike da kambun kasar Aljeriya, ya bayyana cewa kasar Najeriya da za su kara da ita, ta na cikin wadanda a ke gani za su iya lashe gasar cin kofin Nahiyar Afrika na 2019.

Babban ‘dan wasan kwallon kafan na kungiyar Manchester City ya na ganin Super Eagles za su fi kawo masu matsala a Gasan bana a kan kasar Ivory Coast a su ka kara da ita a zagayen baya.

Riyad Mahrez ya kara nuna cewa Najeriya za su ji dadi ganin sun buga wasa a Ranar Laraba inda su ka yi waje da Afrika ta Kudu, yayin da Aljeriya ba ta buga wasanta ba sai kashegari Alhamis.

Hutun kwana guda da Super Eagles su ka samu a gasar zai iya taimaka masu a lokacin da su ka fuskanci Aljeriya a cewar Mahrez. ‘Dan wasan ya bayyanawa gidan jaridar Le Buteur ne a jiya.

KU KARANTA: Abin da ya sa na ke so Najeriya su lashe kofin bana - Musa

A Ranar 13 ga Wata Mahrez ya ke cewa:

”Najeriya su ne ‘yan gaba-gaba a Gasar cin kofin Afrika. Na farko dole mu wartsake da kyau domin ba mu samu hutun da su ka samu na kwana guda ba, bayan nan, sai mu shiga bakin daga.”

A zahirin gaskiya, kamar sauran Takwarori na, ina sa rai za mu kai labari. Mun samu gagarumar nasar kawo yanzu a Gasar AFCON din.” Inji Kyaftin din na Abokan hamayyar Najeriya na yau.

Mai buga gefen saman ya kuma bayyana cewa: ”Mun yi nasara a wasanni da dama, sai a karawar mu da Ivory Coast ne kurum wasan ya kai zuwa ga bugun daga kai-sai mai tsaron gida."

‘Dan wasan gaban ya ce za su yi bakin kokarinsu a karawar da za ayi a Lahadi, 14 ga Watan Yuni, 2019. Mahrez ya ce za su shirya da kyau, kuma za su fito da gaske sai inda karfin su ya kare.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel