Kungiyar Miyetti Allah ta yi magana a kan zargin makiyaya da kisan diyar shugaban Afenifere

Kungiyar Miyetti Allah ta yi magana a kan zargin makiyaya da kisan diyar shugaban Afenifere

Kungiyar Fulani Makiyayan ta Najeriya (MACBAN) ta yi Alla wadai tare da nesanta kan ta daga kisan Funke Olakunrin, diyar shugaban kungiyar 'yan kabilar Yoruba (Afenifere), Dattijo Reuben Fasoranti.

A wani jawabi da ta fitar ranar Asabar a Abuja, mai dauke da sa hannun sakarenta na kasa, Baba Ngelzarma, kungiyar MACBAN ta mika sakon ta'aziyya ga Fasorati a kan rasuwar diyarsa.

Ya ce marigayiyar ta mutu ne ranar Juma'a sakamakon harbinta da da wasu 'yan bidiga suka yi a kan hanyar Kajola zuwa Ore a jihar Ondo kamar yadda rundunar 'yan sanda ta bayyana.

Ngelzarma ya ce, "Muna mika sakon ta'ziyyar mu ga dangin marigayiyar."

Ya kara da cewa kungiyar MACBAN ta yi matukar mamakin yadda wani bangare na kafafen yada labarai da wasu marasa kishin kasa ke kokarin amfani da batun kisan marigayiya Funke domin rura wutar rikicin kabilanci.

DUBA WANNAN: Harin Metele: Rundunar soji ta kori sojoji 8 saboda nuna halin 'farar kura'

Ya bayyana bakin cikin kungiyarsu a kan yadda wasu makiya Fulani ke son ganin an kashe makiyaya ta hanyar dora alhakin duk wani aikin ta'addanci a wuyansu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito.

"Mu na Alla wadai da kafafen yada labarai marasa kishi da ke yada karya a kan makiyaya domin taimaka wa makiya Fulani cimma burinsu na ganin an kashe mutanen mu ta kowacce hanya.

“Mu na kira ga jami'an tsaro da su gaggauta kama wadanda aikata laifin tare da gurfanar da su domin su girbi abinda suka shuka," a cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel