Harin Metele: Rundunar soji ta kori sojoji 8 saboda nuna halin 'farar kura'

Harin Metele: Rundunar soji ta kori sojoji 8 saboda nuna halin 'farar kura'

Rundunar soji ta kori wasu jami'anta 8 daga aiki bayan an zarge su da guduwa daga sansanin su bayan mummunan harin da mayakan kungiyar Boko aram suka kai kan rundunar soji ta 157 a kauyen Metele da ke karamar hukumar Guzamala a jihar Borno.

Sojoji da dama da suka hada kwamanda, Laftanal Kanal Ibrahim Sakaba, sun rasa ransu sakamakon harin da aka kai sansanin sojin a watan Nuwamba na shekarar 2018.

Jaridar Sunday Punch ta rawaito cewa an gano sojoji sun gudu ne bayan an gudanar da kidaya a sansaninsu. Wasu daga cikinsu sun bayyana bayan wata guda da kai harin.

A ranar 19 ga watan Afrilu, mukaddashin kwamandan rundunar soji ta 157, Manjo UI Lezuya, ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano dalilin bacewar sojoji da kuma bayyanarsu daga baya.

Wata majiya daga cikin rundunar soji ta ce binciken da aka gudanar ya hada gano lokacin da sojojin suka bar sansanin, dalilinsu na yin hakan da kuma dalilin dawowarsu bayan shafe kwanaki basa nan da me suke yi bayan a tsawon lokacin da basa sansanin.

DUBA WANNAN: An kama wata 'yar kabilar Igbo da ke yin jabun madarar 'Peak'

Ragoar abinda bincike ya shafa sun hada da gano inda sojojin suka ajiye bindoginsu ko kuma sun dawo tare da su bayan shafe lokaci mai tsawo basa sansaninsu da kuma sanin ko rundunar da suke ciki tayi wani kokari wajen bayar da shawarar a hukunta su bayan sun gano cewar basa nan.

Wata babbar majiya daga cikin mahukunta a rundunar soji ta bayyana cewa kwamitin mutum biyar da aka kafa ya samu sojojin da aikata laifin da ake tuhumarsu da aikata wa, wanda a saboda haka kuma aka kore su daga aiki.

Duk da majiyar ba ta ambaci sunayen sojojin ba, ta bayyana cewa hukuncin ya yi tsauri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel