An kama wata 'yar kabilar Igbo da ke yin jabun madarar 'Peak'

An kama wata 'yar kabilar Igbo da ke yin jabun madarar 'Peak'

Hukumar kare masu amfani da kayayyaki ta kasa (CPC) ta bankado wata haramtacciyar masana'antar hada jabub madarar 'Peak' a kasuwar Eziukwu, Aba, a jihar Abiya.

Jami'an hukumar sun yi nasarar damke wata mata da ke hada jabun madarar kuma ta bayar da muhimman bayanai a kan mutanen da ke taimaka mata wajen sayar da haramtacciyar hajar ta.

Tuni jami'an hukumar suka mika ta hannun jami'an 'yan sanda domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da ita.

Wannan ba shine karo na farko da aka fara samun 'yan kasuwar Aba na kirkirar kayan amfani na jabu ba.

DUBA WANNAN: Abin bakin ciki: Yadda wata budurwa ta hada baki da saurayinta suka yi garkuwa da mahaifinta

Jami'an 'yan sanda da na hukumar kula da nagartar abin ci/sha da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta sha gano haramtattu masana'antun sarrafa ababen ci ko na sha ko kuma magunguna a kasuwar.

Masu kirkirar irin wadannan jabun kaya na jawo wa kamfanoni asarar kudade ta hanyar cushe kasuwa da jabun kayansu, marasa inganci. A wasu lokutan ma, su na amfani da sinadarai masu cutar wa wajen hada jabun kayayyaki.

An kama wata 'yar kabilar Igbo da ke yin jabun madarar 'Peak'

Jabun madarar 'Peak'
Source: Facebook

An kama wata 'yar kabilar Igbo da ke yin jabun madarar 'Peak'

Wurin da suke yin jabun madarar 'Peak'
Source: Facebook

An kama wata 'yar kabilar Igbo da ke yin jabun madarar 'Peak'

'Yar kabilar Igbo da ke yin jabun madarar 'Peak'
Source: Facebook

An kama wata 'yar kabilar Igbo da ke yin jabun madarar 'Peak'

An kama wata 'yar kabilar Igbo da ke yin jabun madarar 'Peak'
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel